Jam’iyyar PDP ta yi kira ga shugabannin gaban kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta kai ziyara kauyes Zabarmari, sannan ya gana da iyalan manoma sama da 40 da Boko Haram suka kashe.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya aika da sakon ta’aziyya ga iyalan manoman da Boko Haram suka ka yi wa kisan a karamar hukumar Jere, jihar Barno.
Tuni dai aka yi jana’izar mamatan da safiyar lahadi.
PDP ta ce aika wa da sako kawai bai isa ba, kamata yayi shugaba Buhari da kansa ya ja zugar manyan jami’an gwamnati su kai ziyara wannan gari kuma ya gana da ƴan uwa da iyalan wadanda aka kashe.
” Matsalar rashin tsaro a kasar nan yayi matukar muni a kasar nan yanzu. Muna ka ra ga gwamnatin APC ta gaggauta samarwa mutane tsaro a fadin kasar nan
Yadda Boko Haram suka kashe manoman shunkafa 44 a jihar Barno
Akalla manoman shinkafa sama da 40 wasu mahara da ake zaton Boko Haram ne suka yi wa kisan gilla a tsakiyar gonakinsu a daidai suna aikin girbi.
Dan majalisar Tarayya dake wakiltar yankin Ahmed Satomi, da aka kai wa hari ya shaida haka yana mai cewa zuwa yanzu an mika musu gawarwakin manoma 44 da aka yi wa kisan gilla a gonakin su, wanda za a rufe ranar Lahadi.
” Manoma da masu kamun kifi 44 da aka kawo mana gawarsu zuwa yanzu. Duka wadannan manoma na aiki ne a wani katafaren gonan shinkafa da ke garin Garin-Kwashebe.
Haka shima shugaban kungiyar Manoman shinkafa na jihar Barno, Hassan Zabarmari ya tabbatar wa PREMIUM TIMES aukuwar wannan mummunar al’amari.
Majiya mai karfe ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa saida maharan suka tattara manoman sannan suka rika bi suna kashe daya bayan daya dukkan su.
Idan ba a manta ba a wannan rana ne ta Asabar, ake zaben kananan hukumomi na jihar Barno, bayan an shafe shekaru 12 ba ayi zaben kananan hukumomi a jihar ba.