Kashi 18.3% na mutanen da Korona ta kashe a Afrika na dauke da ciwon siga – Binciken WHO

0

Sakamakon wani bincike da kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta yi a kasashen Afrika 14 ya nuna cewa kashi 18.3% na mutanen da cutar korona ta kashe a Afrika na fama da cutar siga wato ‘Dibeties’ a daidai lokacin da suka kamu da cutar.

WHO ta gabatar da wannan sakamako a wani takardan da ta bada bayanan shirye-shiryen taron ciwon Siga ta duniya da za a yi ranar 14 ga Nuwamba.

An kebe wannan rana domin wayar wa mutane kai game da ciwon da hanyoyin da za a kiyaye domin guje wa kamuwa da da ita.

Binciken da WHO ta gudanar ya nuna hadarin da masu dauke da ciwon siga ke ciki a wannan lokaci da annobar korona ta dabaibaye duniya musamman ga wadanda ke da shekaru 60 zuwa sama.

An gano cewa mutane da dama da ke dauke da wasu cututtukan sukan fada cikin yanayi na damuwa saboda maida hankali da aka yi kan kauda korona. Wasu cututtukan kuma suna ta cigaba da yaduwa.

Share.

game da Author