KASAFIN 2021: Za a ciyar da yaran makaranta, a basu maganin tsutsan ciki na naira biliyan 142.3

0

Gwamnatin Najeriya ta ware Naira biliyan 142.3 domin ciyarwa da baiwa yaran makaranta maganin tsutsan ciki a kasafin shekarar 2021.

Ma’aikatar Jinkai da Inganta Rayuwa za ta aiwatar da haka a karkashin shirinta na ciyar da yaran makaranta a kasar nan, (NHGSFP).

Gwamnati ta ce za ta yi amfani da wadannan kudade wajen ciyar da yara miliyan 10, baiwa yaran dake aji 1 zuwa 3 maganin tsutsan ciki a jihohi 36 da Abuja, sannan kuma da saka yara 60,000 dake gararamba a tituna makaranta sannan da horas da masu dafa abinci da manoma.

PREMIUM TIMES ta samu wannan bayanai a takardan da hadaddiyar kwamitin kawar da talauci na majalisar dakoki ta gabatar wa majalisar dattawa a Oktoba.

Ma’aikatar ta Kuma ce a shekaran 2021 za ta fadada shirin ciyar da yaran makarantar domin ciyar da yaran miliyan biyar da basu makaranta.

Sannan ta yi amfani da Naira miliyan 2.7 wajen siyo kayan aikin da za a yi amfani da su wajen girka abinci wa yara.

Ma’aikatar Jinkai da Inganta Rayuwa za ta samu wadannan kudade ne daga cikin Naira biliyan 400 zuwa 350 da majalisar ta gabatar domin kula da walwalan ƙasa a 2021.

Kassafin kudin shekara 2021

Ma’aikatar Jinkai da Inganta Rayuwa ta bukaci a ware mata Naira biliyan 4.04 wa a cikin kassafin kudin shekaran 2021.

Idan gwamnati ta amince da haka ma’aikatar za ta samu karin kashi 29 bisa Naira biliyan 3.125 da gwamnati ta ware wa ma’aikatar a kassafin kudin shekaran 2020.

Daga cikin wadannan kudade da gwamnati ta ware a 2020 Naira biliyan 1.2 ne kawai ma’aikatar ta samu a watan Satumba.

Bisa ga takardan da ma’aikatar ta mika wa majalisar dokoki ya nuna cewa ma’aikatar za ta yi amfani da Naira miliyan 796.5 a hidimomin yau da kulun, ta biya albashin ma’aikata da Naira miliyan 296.5, ta kashe Naira miliyan 3.24 wa manyan hidimomi.

Daga cikin wadannan kudade Kuma ma’aikatar za ta yi manyan hidimomi guda 32 wanda daga ciki ma’aikatar na Kan aiki akan guda 29 sannan za ta kirkiro wasu sabbi uku.

Share.

game da Author