Jam’iyyar PDP ta yi kira da Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta janye karin kudin fetur, wanda aka yi daga naira 159 zuwa naira 170.
Kakakin Yada Labarai na jam’iyyar PDP, Kola Olagbondiyan ne ya fitar da sanarwar da ke dauke da wannan bayani a ranar Juma’a da yamma.
Sanarwar wadda aka fitar daga hedikwatar PDP da ke Abuja, ta ce wannan kari ba zai karbu ga jam’iyyar da sauran al’ummar Najeriya.
Olagbondiyan ya kara da cewa ba fa za a yarda da wannan karin kudin litar man fetur ba, idan aka yi la’akari da irin halin matsi da kuncin da a kullum jama’a ke fama da su.
Wannan kari a cewar Kola, zai kasance wani babban nauyi aka kara dora wa ‘yan Najeriya, bayan an yi masu alkawarin kara samun saukin rayuwa.
Daga nan sai ya ce babu wata hujja ko dalilin da zai sa gwamnatin Buhari ta rika sayar da fetur sama da naira 100, ballantana kuma a ce zai koma naira 170.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin karin kudin litar fetur. Ta kuma bada labarin cewa farashin litar fetur ya koma naira 172.
‘Yan Najeriya za su tashi da shirin gyara da kimtsin fara sayen litar fetur naira 172 zuwa naira 175 a gidajen mai, ganin yadda wata sanarwa ta fitar da karin farashin yadda ake sayar wa masu gidajen mai kowace lita daga daffo.
Wata sanarwa da PREMIUM TIMES ta gani ta tabbatar da sanar da karin kudin litar fetur daga daffo ga dillalan mai masu gidajen mai, daga naira 147 zuwa 155.17 kowace lita.
Hakan kuwa ya na nufin za a rika sayar da lita daya ta fetur a gidajen mai daga naira 168 har zuwa naira 172 ko naira 175.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Ali Tijjani na Hukumar Kayyade Farashin Fetur, an fitar a ranar 11 Ga Nuwamba, idon PREMIUM TIMES ya leko cewa karin zai fara tun daya ranar Juma’a, 13 Ga Nuwamba.
Tijjani ya bayyana cewa karin ya zama wajibi ne saboda karin kudin ladar saukalen fetur daga cikin jiragen ruwa a tashoshin jiragen ruwa.
Ya ce a cikin watannin Satumba da Oktoba gwamnati na biyan naira 119 ladar saukale, amma yanzu ana biyan naira 123 a cikin Nuwamba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa tsadar fetur ta kori motocin Shugabancin Kasa, Ministoci da na kamfanin Dangote sun koma amfani da gas.
Rahoton ya nuna motocin Buhari, Ministoci da tirelolin Dangote sun koma amfani da gas, kuma Karamin Ministan Fetur ne ya bayyana wa PREMIUM TIMES haka a ofishin sa.
Karamin Minstan Man Fetur Timiprey Sylva, ya bayyana cewa tsadar fetur ya sa an maida dukkan motocin ofishin sa amfani da gas, kuma ana kan maida na Ofishin Shugaba Muhammadu Buhari, na Ministoci da na Majalisar Dattawa da ta Tarayya zuwa amfani da gas.
Da ya ke tattaunawa sa PREMIUM TIMES a ofishin sa, Minista Sylva ya ce tuni manyan tirelolin kamfanin Dangote ma duk sun koma amfani sa gas.
“Kuma an shaida min a yanzu haka kamfanin na Dangote na samun saukin kashe kudaden shan mai da kashi 50 bisa 100. Wato a yanzu rabin abin da ake kashe wa motocin ga fetur ne ke isa a sayi gas.
Minista ya ce wannan ce mafitar samun sauki, kuma nan da ranar 30 Ga Nuwamba, 2020 za a kaddamar da shirin a kasa baki daya.
Wannan bayani ya zo daidai lokacin da farashin mai ya tashi daga naira 161 ya koma naira 170.
‘Yan Najeriya na ta tofin Allah wadai da karin fetur din da za a fara dandanawa daidai karshen shekara.
Da ya ke magana, Sylva ya ce an zo lokacin da za a daina dogaro da fetur a matsayin abin zuba wa mota, saboda tsadar sa.
Ya kuma yi kukan cewa duk da Najeriya na sahun farko na kasashe masu arzikin gas a Afrika, ya ce har yanzu ba a amfani da gas sosai a Najeriya, sai dai a birane da manyan garuruwa kadai.
“Mun kammala tattaunawa da Ministoci dangane da maida motocin su masu amfani da gas. Su ma Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya, za mu zauna da su, domin tattauna batun maida na su motocin gaba daya masu amfani da gas, domin ya fi sauki sosai. Inji Sylva.
Discussion about this post