Kamfanin Saida Lantarki na AEDC ya bayyana cewa ya rage kudin wutar lantarki ga wadansu rukunin matakan masu amfani da wutar da su ke sha daga kamfanin su, daga ranar 1 Ga Nuwamba.
Babban Manajan Sadarwa na AEDC, Oyebode Fadipe, ya shaida cewa ragin ya fara daga Lahadi, 1 Ga Nuwamba, ranar da ya yi jawabin.
“Mu na sanar da kwastomomin my cewa daga ranar 1 Ga Nuwamba, mun rage tsarin farashin kudin wuta, wato ‘Service Regulative Tariff.”
Fadipe ya ce duk kwastomomi masu amfani da mita, su ne za su fara amfana da ragin.
“Su kuma wadanda ba su da mitar, to za su ga ragin kudin da aka yi masu a cikin ‘bill’ din takardar biyan kudin wutar da su ke sha.
“Mun kasa masu sayen wuta zuwa rukuni biyar. Kuma rukunin da kowa ya ke, ya danganta ne a yawan wutar da ake tura wa yanki ko unguwar da ya ke, da kuma sa’o’in da unguwanni ke samun wutar.
“Kwastomomin da ke kan rukuni na D da E, ba a yi masu kari ko ragi ba.
“Kwastomomin da ke kan rukunin A, B da C za su ga ragin da aka yi masu daga ranar 1 Ga Nuwamba.”
Ya ce AEDC ta jajirce kan ci gaba da kyautata wa kwastomomin ta, kuma za ta kara lokutan da ta ke bayar da wuta sosai.
Ya ce nan ba da dadewa ba AEDC zai fitar da jadawalin ragin kudaden domin duk wanda zai amfana da ragin ya gani.