Wani likitan mata mazaunin jihar Legas mai suna Wale Farayola, ya ce a duk lokacin da mace ta ga jinin al’adarta na wuce lokacin da ya kamata ya yanke, ta gaggauta zuwa asibiti domin hakan alama ce ta Kaban Ciki.
Kaban ciki cuta ce da kan tsira wa mace a mahaifa, kuma a yakan jikkirta lokacin da take fara haila da kuma tsayawar sa.
Alamun cutar sun hada da kwararan jini lokacin haila, fama da ciwon mara mai tsanani ko a lokacin da ake haila.
Farayola ya ce kaban ciki kan yi girma kamar da a mahaifar mace.
Ya ce idan haka ya faru kamata ya yi a nemi magani ko kuma a yi fida a cire shi.
A karshe likta Farayola, ya ce shan magani kadai baya hana shi tsira koda ya mutu, sai dai idan an yi fida an cire shi, yakan iya sa ba za a sake tsira ba.
Kira da gargadi ga mata
Wani likita dake aiki da asibitin Calvary Estate dake garin Benin, jihar Edo, Osas Ikponwonsa ya yi kira ga mata da su rage yawan shan magungunan musamman wadanda ke dauke da sinadarin ‘Estrogen’ domin guje wa kamuwa da kabar ciki.
Osas ya bayyana cewa ‘Estrogen’ sinadari ne dake taimakawa wajen kara wa farjin mace mata da wasu bangaron jikin ta lafiya. Sannan wannan sinadarin ya fi yawa a kwayoyin hana haihuwa.
Sannan kaban ciki cuta ce dake fito a mahaifar mace wanda idan ba a gane da wuri ba ke iya hana mace haihuwa.
Osas ya ce har zuwa yanzu likitoci basu gano abin dake kawo wannan cuta ba saidai bincike ya nuna cewa yawan amfani da magunguna na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
” Yawan rashin lafiya a lokacin da mace ke haila, yawan zuban jini a lokacin haila, ciwon ciki, jin nauyi a mara da sauran su na cikin alamun wannan cuta.
Osas ya ce bincike ya nuna cewa kashi 20 zuwa 50 na matan dake a duniya na dauke da wannan cuta. Sannan wasu matan kafin su kai shekarun gama haihuwa kashi 30 zuwa 77 daga cikin sukan kamu da wannan cuta a duniya.
A dalilin haka Osas yake kira ga mata da su guji shan magani batare da izinin likita ba musamman wadanda ke dauke da sinadarin ‘Estrogen’ domin gujewa kamuwa da cutar.
Discussion about this post