Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yanke shawarar gudanar da zabubbukan cike gurabu guda 15 da su ka rage a ranar 5 ga Disamba.
Babban Kwamishina kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zabe a hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya bayar a Abuja, ya na mai bayyana cewa an yanke shawarar hakan ne a taron da kwamitin ya yi a ranar Juma’a.
Ya ce daga cikin abubuwan da INEC ta duba har da zaman tuntuba da ta kan yi da masu ruwa da tsaki a harkar zabe a duk bayan wata uku.
Ya ce hukumar ta sake nazarin yanayin tsaro da sauran matsaloli da su ka shafi zabubbukan cike gurabun da za a yi a jihohi 11.
A ranar 22 ga Oktoba ne hukumar ta ɗage gudanar da zabubbukan cike gurabun da ta shirya yi a ranar 31 ga Oktoba saboda yanayin tsaro da sauran matsalolin sauyin yanayi da ke addabar kasar nan.
Okoye ya tunatar da cewa hukumar ta sake zama a ranar 5 ga Nuwamba kuma ta sake nazarin halin da ake ciki.
Ya ce a zaman, hukumar ta yi la’akari da cewa daga cikin abubuwa da dama akwai barnar kayan da aka yi a ofisoshin ta da ke kananan hukumomi wanda ya shafi wasu sassa inda za a yi zabubbukan cike gurabun.
Ya ce, “Don haka, hukumar ta yanke shawarar ta tuntuɓi muhimman masu ruwa da tsaki a harkar zabe kafin ta yanke shawarar sake saka ranar da za a gudanar da zabubbukan.
“Hukumar ta tuntubi jam’iyyun siyasa da kungiyoyi masu zaman kan su a ranar 10 ga Nuwamba, da kuma kafafen yada labarai da kwamitin tuntubar hukumomin tsaro kan batun zabe, wato ‘Inter-Agency Consultative Committee on Election Security’ (ICCES) a ranar 11 ga Nuwamba.
“A karshe, ta yi taro da kwamishinonin zabe na jihohi a ranar Alhamis, 12 ga Nuwamba.
“Bisa ga wadannan tuntuɓa da aka yi, hukumar ta yi amanna da cewa an samu ingantuwar samar da tsaro a jihohin da abin ya shafa sannan matsalolin yanayi ma sun ragu bakin gwargwado.
“Don haka, hukumar ta yanke shawarar ta gudanar da dukkan zabubbukan da su ka rage a ranar Asabar, 5 ga Disamba.”
Babban kwamishinan ya ce INEC ta yi godiya kan goyon baya da fahimta da kuma hadin kan da masu ruwa da tsaki da dukkan jama’a su ka ba ta a lokacin da ta ke shawarwarin sake saka ranar da za a yi zabubbukan cike gurabum.
A cewar sa, an yi hakan a bisa yunkurin da ake yi na sauya fasalin harkar zabe da kuma okarin ganin an bada ma’ana da daraja ga kuri’un masu zabe.
Okoye ya kuma yi kira ga masu zabe da masu ruwa da tsaki a jihohin da za a yi zabubbkan da su ci gaba da bada haɗin kai ga INEC a ƙkokarin ta na gudanar da zabubbuka masu inganci a yanayin tsaro mai kyau.