Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce za ta soma wani sabon aikin yi wa masu zabe rajista a cikin watanni uku na farko na shekarar 2021.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja a ranar Laraba bayan ya bayyana a gaban Kwamitin Hukumar Zabe ta Ƙasa na Majalisar Dattawa domin ya kare kasafin kudin hukumar na shekarar 2021.
A cewar sa, za a yi aikin yin rajista har zuwa watanni shida kafin a yi manyan zubukan shekarar 2023.
Ya ce, “Za mu ci gaba da gudanar da aikin yin rajistar masu zabe a watanni uku na farkon shekarar 2021. Kuma da zarar mun ci gaba, aikin zai ci gaba babu tsayawa har zuwa shekara daya da rabi, akalla watanni shida kafin a yi manyan zabukan da ke gaba.”
Haka kuma ya bayyana cewa a yanzu haka hukumar ta na fafatawa a kararraki kamar 1,700 na kafin zabe da bayan zabe da aka kai kotu daga zabukan shekarar 2019.
Sai dai kuma ya ce hukumar ba ta biyan lauyoyi manyan kudaden shari’un da ake yi amma ta na dai biyan kudaden da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya ta kayyade.
Farfesa ya ce, “Misali, idan mu na da shari’a daga zaben gwamna a Kotun Koli, kudi mafi yawa da za mu biya lauyoyi shi ne naira miliyan 4.5, amma saboda yawan shari’un mun kusa samun ƙararraki har guda 1,700 na kafin zabe da na bayan zaɓen shekarar 2019 kadai.
“A ko yaushe za ka ji mutane su na zuwa kotu tare da haɗa INEC a karar su, amma mu dai za mu ci gaba da yin abin da za mu iya ne da iyakar abin da ke aljihun mu.”
Tun da farko a jawabin sa ga Majalisar Dattawan, Farfesa Yakubu ya ce hukumar ta tsara za ta ɗauko kudi naira biliyan 5.2 daga asusun ta na naira biliyan 10 ta hada cikin kasafin ta na shekarar 2020.
Ya ce hukumar ba ta taba kashe ko kwabo ba daga wannan asusun tun da aka kafa ta a cikin 2010, yayin da ya ce dalilin da zai sa a ciro kuɗin shi ne saboda rage mata kudi da aka yi a kasafin shekarar 2020.
Ya ce, “Abin da ya faru yanzu shi ne kasafin mu na shekarar 2020 ya yi kasa da naira biliyan 40 daga naira biliyan 45.5 a shekarar 2019.
“Saboda kashi 10 cikin ɗari na kudin da aka zabtare saboda annobar korona, sai kuma kudin su ka kara raguwa zuwa naira biliyan 36 a tsakiyar shekarar a lokacin da mun riga mun gama shirye-shiryen kashe kudaden.
“Saboda haka, tunda dai an yi asusun ne saboda lokaci irin na yau da ake bukatar sa, na sanar da kwamitin cewa ranar bukatar kudin ta zo.
“Don haka, za mu ciri wani sashe na kudin asusun domin mu yi balas da kasafin mu na bana.”
A kan batun bai wa ‘yan Nijeriya mazauna kasar waje damar yin zabe a inda su ke, shugaban ya ce hakika hukumar ta na son ganin ta ba su dama su yi zabe, amma tabbatar da yiwuwar hakan ya na bukatar a yi wa tsarin mulki da kuma Dokar Zabe garambawul.
Ya ce, “Mun riga mun gama tsara takardun, da zarar an gyara dokar, to za mu iya fara aiwatarwa.
“Mun gama shiri, mun yi zama da dama da su ‘yan Nijeriya a Hukumar Mazauna Ketare, wato Diaspora Commission (NIDCOM), amma ba za mu iya tsallake abin da doka ta tanadar ba.”