INEC: Kwamitin Majalisa zai yi zaman tantance karin wa’adin Farfesa Yakubu a karo na biyu

0

Kwanaki biyu bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya roki Majalisar Dattawa ta daga wa Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa kafa, ta amince da shi a karo na biyu, Kwamitin Harkokin Zabe zai yi zama tare da Farfesa Yakubu a yau Alhamis.

Shugaban Kwamitin Sanata Kabiru Gaya, ya bayyana wa manema labarai cewa kwamitin zai zauna ranar Alhamis karfe 2:00 na rana.

Sanata Gaya ya ce Shugaba Buhari ya sake aika masu da sunan Yakubu karo na biyu, kuma ya sake rokon su tantance shi.

“Saboda da haka a ranar Alhamis kwamitin mu zai gayyace shi a zauna karfe 2:00 daidai na rana. Kuma daga nan sai kwamitin ya mika wa Majalisar Dattawa rahoton batun sake sake amincewar da shi domin ya shugabanci INEC a karo na biyu.

Shugaba Muhammadu Buhari ya buƙaci Majalisar Dattawa da ta amince da zabin sa na Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) don yin wa’adi na biyu.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa Shugaban majalisar, wato Sanata Ahmad Lawan, wadda aka karanta a zauren majalisar a ranar Talata, Buhari ya ce, “Bisa la’akari da sashe na 154 (ƙaramin sashe na 1) na Kundin Tsarin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya (wanda aka gyara), ina farin cikin gabatar wa da Majalisar Dattawa da Farfesa Mahmood Yakubu don a tabbatar masa da yin wa’adi na biyu.”
 
Shugaban Kasar ya ce ya na sa ran za “a gaggauta duba” wannan bukata tasa.
 
Idan an tuna, kwanan baya ne Buhari a cikin wata sanarwa ya bayyana zaben Yakubu domin yin wa’adi na biyu a matsayin Shugaban INEC.

Shi kuma Yakubu, kwanan nan ya ja baya daga shugabancin hukumar saboda wa’adin sa ya cika, ya dakanci Majalisar Dattawa ta sake tabbatar masa da nadin nasa.

Share.

game da Author