Wata matar malamin dake koyarwa a kwalejin kimiya da fasaha dake Itori jihar Ogun Maimunat Mufutau ta bayyana cewa ta ji labarin mutuwar mijinta ne a yanar gizo amma kafinnan ba ta san ya rasu ba.
Waliu Mufutau mijin Maimunat na aiki da kwalejin kimiya da fasaha dake Itori a jihar Ogun.
Mufutau mai shekaru 35 dan asalin karamar hukumar Saki ta Yamma ne kuma yana koyarwa a sashen hada na’urar dake aiki da wutan lantarki ne a makaranta.
Mufutau ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake fitowa daga kwalejin inda wasu mahara a cikin mota suka bindige shi haka kawai a bakin kofar makarantan.
Likitan babban asibitin Ijaye dake Abeokuta ne ya tabbatar Mufutau ya mutu.
Kakakin kwalejin Yinka Adegbite, ya tabbatar da haka yana mai cewa kwalejin ta hada hannu da rundunar ƴan sanda domin gano mutanen da suka kashe shi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abimbola Oyeyemi ya ce ga dukkan alama wani ne ya aiko a kashe Mufutau.
Oyeyemi ya ce rundunar na gudanar da bincike domin kamo mutanen da suka kashe Mufutau.
Yadda na samu labarin mutuwar mijina a yanar gizo
Maimunat ta ce a yanar gizo ne ta ga hotunan mijinta cewa ya rasu.
Ta ce a ranar Talata bayan mijinta ya rasu mutane na ta kiranta ta wayan salula domin yi mata gaisuwa amma da yake bata san me ke faruwa ba, bata iya ganewa ba.
Maimunat ta ce ta gana da mijinta na karshe ranar Litini da yamma domin shi ne ya ke kai ta wurin aiki kullum kuma ranar na shine ya kai ta.
Ta ce idan tana aikin dare Mufutau ne ke kula da ‘ya’yan su sannan idan ta dawo da safe ta karbe shi.
Ta ce da za ta dawo gida a safiyan Talata ta yi waya da shi inda har ya aiko mata kudin cefane Naira 2,000.
Maimunat ta ce da mijinta bai amsa wayar salulan sa ba da yammacin Talata sai bata damu ba domin tana tunanin zai dawo gida.
Ashe tuni wasu sun aika da shi lahira. Daga nan ta kira hukumar makarantar da ƴan sanda.
Discussion about this post