Kodinatan Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da cutar Korona, Sani Aliyu yayi kira ga ‘Yan Najeriya su hakura da tafiye-tafiye a wannan lokaci idan ba aya zama dole ba.
Aliyu ya ce gwamnati ba za ta sassauta dokar Korona ba sannan ya kara da cewa duk dokokin da aka saka haka za a ci gaba da kiyaye su a yanzu da aka tunkari bukukuwan kirsimeti.
” Hankalin mu ya tashi a Najeriya yanzu ganin yadda cutar ke hauhawa a kasashen duniya yanzu. Dole mu cigaba da sa ido da kuma samar da duk kariyar da ya kamata domin kada muma mu sake afkawa cikin matsalar Korona a karo ta biyu.
Ya roki ‘yan Najeriya su yi hakuri da tafiye-tafiye a wannan lokaci musamman saboda bukukuwan kirsimeti.
Haka kuma shi ma shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu, ya gargadi matafiya da su su dan saurara da tafiye-tafiye a wannan lokaci.
Chikwe Ihekweazu, ya kara da cewa baya ga Korona da ya ke neman dawowa sabo yanzu, a kwau cututtukan Ebola, Zazzabin Shawara da ke addabar mutane yanzu wanda dole a yi kaffa-kaffa yan zu tunda wuri.