Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya yi kira ga ƴan Najeriya cewa idan ba su gamsu da ƴan Majalisar da ke kan wakilci a yanzu ba, to su musanya su da wasu idan zaɓen 2023 ya zo.
Lawan ya yi wannan duruci a ranar Juma’a, a lokacin wani taron manyan ma’aikatan Majalisar Tarayya da ma’aikatan Hukumar Kula da Majalisar Tarayya, a Abuja.
Wannan bayani na sa ya zo ne a lokacin da ƴan Najeriya da sauran kungiyoyi ke ci gaba da yawan sukar shugabanni, ciki kuwa har da ƴan Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.
Lawan ya nuna cewa ya na ganin laifin ƴan Najeriya masu hakikicewa su sai sun ga yawan kasafin kudin Majalisa, maimakon su maida hankula wajen ganin ayyukan da aka ce an yi, shin an yi su din ko kuwa ba a yi ba?
Ya ce maimakon a yi ta mahawara kan a rushe majalisun biyu, ko tankiya kan yawan albashin da ake biyan su, kamata ya yi a tsaya a yi magana kan abin da za su fi maida hankali a kai da zai di amfanar ‘yan Najeriya.
“Shin wai kun kuwa san gagarimar matsalar da za a rufta idan aka rushe Majalisar Dattawa? Ba wai don ina Majalisa ba ne na yi maku wannan tambaya.
” To Majalisar Dattawa ba kamar ta Tarayya ba ce, domin ita ta Tarayya, gwargwadon yawan jiha gwargwadon yawan mambobin tarayyar ta. Amma ta Dattawa duk kankantar yawan al’ummar Bayelsa, sanatoci uku gare ta, kamar yadda duk yawan jama’ar jihar Kano, sanata uku ita ma ta ke da shi.”
Ya ce ba ya na magana don ya kare “yan majalisa ba ne. “Shi ya sa ma na ce idan jama’a ba su gamsu da zubin na yanzu ba, to idan zaben 2023 ya zo, su canja su.”