Hukumar UBEC za ta tura malamai 3,700 makarantun jihohin kasar nan da Abuja

0

Gwamnatin tarayya ta ce za ta aika da malamai 3,700 zuwa makarantun jihohin kasar nan da Abuja.

Za a aika da malaman ne bayan an kammala koyar da su ilimin Komfuta ta yadda za su rika koyar da dalibai wannan fasaha.

Shugaban hukumar kula da ilimi Firamare ta Kasa (UBEC) Hamid Bobboyi, ya sanar da haka da a lokacin da ya ziyarci wuraren da malaman ke daukan darasi da rubuta jarabawar a Abuja ranar Litini.

Ya ce jarabawar na gudana ne a ofisoshin JAMB dake fadin kasar nan.

A Abuja jarabawar na gudana a ofisohin hukumar JAMB dake Kogo da Bwari.

Gwamnati na gudanar da wannan jarabawa ne domin zakulo kwararrun malaman da za su rika koyarwa sannan da kawar da matsalar karancin malamai a makarantun kasan.

Bobboyi ya ce malamai 14,729 ne suka rubuta jarabawar inda daga cikinsu ne za a zabi 3,700 wadanda suka yi nasara a jarabawar a tura su makarantun.

Ya ce za a tura su koyarwa a makarantun dake karkara.

Bayan haka, Babboyi yayi karin bayani game da karancin malamai da kasar ke fama da shi. Ya ce makarantun kasar nan na bukatan karin yawan malamai.

Ya ce zuwa yanzu akwai akalla malamai miliyan 1.4 dake koyarwa a makarantun kasar.

Ya ce a yanzu haka akwai yaran makaranta akalla miliyan 42 a kasar nan wanda kuma yawan su ke karuwa a kullum.

Cibiyar kula da aikin malaunta ta kasa TRCN ta bayyana cewa za ta yi wa malamai 17,602 jarabawar kwarewa a aiki a kasar nan.

Shugaban Cibiyar Josiah Ajiboye ya ce daga cikin wadanda za a yi wa jarabawar jihar Ogun na da mutum 1,727, Adamawa na da mutum 1,623, Nasarawa 934 sannan Abuja 850.

Share.

game da Author