Hukumar Tace Fina-finan Hausa ta Jihar Kano za ta kutsa YouTube don banƙado masu karya doka

0

Hukumar Tace Fina-finan Hausa ta jihar Kano ta ce za ta fantsama cikin dhafukan YouTube na yanar gizo domin yin farautar masu saka fina-finai da suka karya dokar hukumar.

Shugaban Hukumar, Isma’ila Na’abba ya shaida cewa hukumar ta gano cewa masu shirya finafinai suna fakewa da wannan dama domin kauce wa sharuddan hukumar.

” Mun gano wasu masu shirya finafinai na kauce wa dokokin hukumar suna saka fim batare da hukumar ta tace su ba. Sannan hakan ya basu daman saka duk abinda suka ga dama, har da wadanda dokar hukumar bata amince da su ba.

Afakallahu ya kara da cewa daga yanzu hukumar zata dira shafukan yanar gizo, wato shafin YouTube domin farautar ire-iren wadannan fina-finan.

Share.

game da Author