Hukumar BCDA ta ce dumbuza kuɗaɗen aljifan ma’aikata ba laifi na ne, duk da dokar ƙasa ta haramta

0

Hukumar Kula da Kan Iyakokin Najeriya, BCDA ta ce duk da dokar kasa ta ce duk da dokar kasa ta haramta gabzar kudaden gwamnati ana kimshewa asusun bankunan ma’aikata, to ita dai kudaden da ta tura aljifan na ta ma’aikatan halastaccen aiki aka yi da su.

BCDA ta ce don haka labarin da PREMIUM TIMES ta buga cewa an karkatar da kudaden hukumar ta hanyar da ba ta dace ba, to ba gaskiya ne.

Hukumar BCDA dai na karkashin wani surikin Shugaba Muhammadu Buhari.

Dokar Najeriya ta Sashe na 713 cikin Kundi na 7 ta haramta kwasar kudin gwamnati a kimshe aljifai ko asusun ajiyar ma’aikatan gwamnati.

Kuma dokar ta ce ko ma da wane dalili ne aka tura kudaden, to an aikata babban laifin da sai hukunci ya hau kan duk mai hannu a cikin harkallar.

Cikin wani bayani da kakakin hukumar mai suna Sadiq Isa ya fitar, ya ce dangane da bukatar da PREMIUM TIMES ta yi a neman ganin kwafen takardun shiga da fitar kudade, ai BCDA ta tura wakilan ta biyu ofishin jaridar, domin su yi wa wakilin ta karin bayani.

Sai dai kuma da wakilan su ka je ofis din, sai su ka kama dawurwura, ba su amsa takamaimen abin da PREMIUM TIMES ta tambaya ba.

Dangane da wani rahoton harkallar da aka taba yi a hukumar a baya kuma, Isa y ace “’Yan Majalisar Tarayya na da ikon tura kudaden su na ayyuka ko a wane asusun ajiya.”

sai dai kuma Isa ya kara bada cikakkar amsar ragargazar da ICPC ta yi wa hukumar BCDA inda ta ce hukumar ta hada baki da wasu ‘yan majallisar tarayya sun karkatar da bilyoyin kudade.

ICPC ta bayyana SMEDAN da BCDA cewa “wasu bututu ne kawai wadanda ake zurara bilyoyin kudin gwamnati, sai a sheka a guje a tara can gaba idan suka zuba kasa a kwashe.”

Binciken PREMIUM TIMES ya tabbatar cewa a cikin kasafin 2018, ‘yan majalisar tarayya sun kudunduna ayyukan raya karkara na bige har guda 391 sun kimshe a cikin kasafin.

Haka ma a cikin kasafin 2019, sun sake banka ayyukan babarodo har sama da 300 a cikin kasafin hukumomin SMEDAN da BCDA.

A Kula: PREMIUM TIMES na nan kan abin da ta buga dangane da harkallar da aka dankara a hukumar BCDA.

Share.

game da Author