HIMMA DAI MATA MANOMA: Babban ƙalubalen da na ke fuskanta a gona – Janet Iliya

0

Wata mata mai suna Janet Iliya mai himmar noma, ta shaida wa wakilinmu cewa ta na da makekiyar gona bakin gwargwado, amma rashin jari mai kauri ya sa ba ta iya fadada noman na ta.

A jihar Neja wakilin mu ya yi kacibis da Janet, inda ya ji ta bakin ta dangane da irin kokarin ta duk kuwa da rashin karfin jarin da bai hana guyawun ta sarewa ba.

Ta bayyana cewa dawa ta ke nomawa, kuma ta gaji gonar ce daga wajen mahaifin ta bayan ya mutu.

A tsawon shekaru biyar da ta yi ta na noma, ta ce gonar za ta kai fadin hekta daya da wani abu.

Ta kara dq cewa daga shirin bunkasa noman karkara na ta ke samun irin shuka.

Janet ta bayyana cea ta zabi noma dawa ce saboda ta fi sauki da saurin sayuwa idan ta tashi sayarwa a kauye. Sannan kuma kasar gonar da ke nomawa ta fi karbar dawa.

Haka kuma ta yaba irin shukar da ke samun tallafin karba ta noma. Sai dai kuma ta ce ba ta amfani da na’urorin noma kamar tarakta da sauran su, saboda gonar ta ba wani girma sosai ta ke da shi ba.

Kana kuma ta ce ba ta ma da kudin da za ta iya sayen kayan noma na zamani ko kuma ta biya ta karba haya.

A cewa Janet, da ya ke ita karamar mai noma ce, bai fi ta noma buhu bakwai ko shida ko ma biyar a shekara ba.

Yayin da ta ce ba ta da wurin adana kayan gonar ta, sai ta ce a dakin ajiye tarkace kawai ta ke amfani da shi.

An tambaye ta yadda ta ke yin noma. Sai ta ce ‘yan uwan ta na taya ta, kuma ta na kiran yara su yi mata noma ta biya su.

Amma kuma ta ce gaba dayan abin da ta ke nomawa duk sayarwa ta ke yi, ba ci ta ki yi ba.

“Ba dauka na ke ina kaiwa kasuwanni na nesa ba. Ina kaiwa kasuwannin kusa da gida ne, saboda ba abu ne mai yawa nake nomawa ba.” Inji Janet.

Ta ce wanda ya rage ba ta sayar ba, sai ta kimshe a cikin buhunna a barbada masu maganin kashe beraye, don kada su cinye mata.

Sai dai kuma Janet ta ce ba ta samun wani tallafi daga gwamnati.

Sannan ta kara da cewa manoma maza ba su nuna mata wani bambanci, kuma ba a taba cin zafarin a gona don ta na mace ba.

“Babbar matsala ta rahin karfin jari, saboda wani lokaci ma hatta kudin maganin kashe kwari da na sayen buhunnan da zan adana kayan gonar, duk gagara ta su ke yi. haka ma takin zamani ya fi karfi na.

Ta ce idan da za ta samu karin karfin jari, to har kayan noma na zamani idan ta samu, za ta iya saye ko ta karbi haya ta na amfani da su.

Share.

game da Author