Harkar kiwon kaji ka iya durkushewa cikin watan Janairu -inji masu kaji

0

Shugaban Kungiyar Masu Kiwon Kaji na Kasa, Emmanuel Ibrahim, ya bayyana cewa idan gwamnati ba ta magance gagarimar matsalar tsadar abincin kaji da wuri ba, to wannan matsalar za ta iya durkusar da harkoki da hada-hadar kiwon kaji a kasar nan.

Da ya ke magana da manema labarai a Abuja, Ibrahim ya ce baya ga tsadar kayan abinci, akwai matsaloli da dama wadanda gwamnati ce kadai za ta iya bijirowa cikin hanzari ta magance su, kafin harkokin kiwon kaji su karye cikin watanni biyu.

Hakan kuwa idan ya faru, shugaban na masu kiwon kaji ya ce abin zai shafi tabarbarewar arzikin dimbi jama’a a kasar nan.

“Kun ga dai farkon bullar cutar korona an hana zirga-zirga, wadda ta shafi kiwon kaji, saboda an daina jigilar kwayayen kaji da jirajiran kaji da kayan abincin kaji. Sanadiyyar haka an tafka asara mai tarin yawan da ta gurgunta jarin masu kiwon kaji a kasar nan.

“An yi asarar bilyoyin nairori daga asarar kaji, kwayayen kaji da abincin kaji. Wasu masu kiwoj kaji sun daina sana’ar, saboda jarin su ya karye.

“Sannan kuma farashin abincin kaji ya tashi daga tan daya naira 95,0000 zuwa naira 164,000.

Ya ce hetrik tan 5,000 da gwamnati ta sayar masu a faraahi mai rahusa bai ishe su ba, saboda matsalar rashin tsaro da ake fama da ita, sai kuma mummunan halin masu boye kayan abinci, domin su fito da shi su sayar idan ya yi tsada.

Ibrahim ya kara da bayyana matsalar karancin waken soya a kasuwa da kuma yadda ya yi tsada, daga nairq 215,000 zuwa naira 250,000.

Ya yi nuni da cewa harkar kiwon kaji babbar harkar kudi ce ta ake sarrafa akalla naira tiriliyan 10, tare da samar wa akalla mutum milyan aahirin hanyoyin samun kudi da samun aikin yi.

Yayin da ya ke kawo shawarwarin da ya ke ganin za a iya bi a fita, Ibrahim ya roki gwamnati ta bada iznin a rika shigo da masara da kuma waken soya daga wake zuwa cikin kasar nan.

Share.

game da Author