HARKALLAR MAINA: Yadda Maina ya lunkume naira biliyan 14 kudin ƴan fansho ya tsuke baki ya yi shiru

0

Wani mai gabatar da kara ya bayyana wa kotu yadda tsohon shugaban, Kwamitin Tattalin gyara tsarin biyan Fansho na kasa, (PRTFT), Abdulrasheed Maina, wanda ke fuskantar shari’a a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya handame kimanin Naira biliyan 14 daga asusun fansho ta hanyar biyan kudade ba bisa ka’ida ba ga ƴann fanshon karya, sannan kuma da bada kwangilolin karya don yi sama da fadi da kudaden hukumar.

Mai bada shaida Roukayya Ibrahim, wanda mai bincike ce na Hukumar EFCC ta fada wa Mai Shari’a Okon Abang, yadda tsohon Shugaban Ma’aikata, Stephen Oronsaye, ya taimaka wa Maina wajen karkatar da wasu kudaden da aka sace ta asusun banki 66.

Hukumar ta EFCC na tuhumar Maina, wanda yanzu haka ya na boye ba a san inda yake ba, tare da kamfanin sa, mai suna ‘Common Input Property and Investment Ltd’ a kan tuhume-tuhume 12 na aikata almundahana da asusun bankuna na karya, cin hanci da rashawa, da kuma halatta kudaden haram na kimanin naira biliyan biyu.

Mai shari’a Abang ya bayar da umarnin ci gaba da shari’ar ne ba tare da Maina ba, bayan ya kasa halartar zaman kotun tun ranar 29 ga Satumbar wannan shekarar, inda lauyan sa, Francis Oronsaye ya ce wanda yake karewa ba shi da lafiya ne yana na a kwance.

A zaman kotun, mai binciken, wanda shi ne shaida na tara da ke gabatar da kara, ya fada wa kotun cewa an gano wani bangare na zargin zambar a shekarar 2010, bayan an gayyaci hukumar EFCC ta shiga aikin yin bincike da tabbar da korafin da ake yi kan badakalar daka tafka a hukumar na fansho.

Mai bada shaida ya ce an gano wasu asusun ajiya da aka rika jibga kudaden ƴan fanshon da ba na gaske bane. An rubuta sunayen karya ne kawai ana ta tula musu kudi, kudaden kuma na shiga asusun Maina.

Sannan kuma bincike ya nuna yadda Maina ya saka kudi a wasu asusun ajiya mallakin Oronsanye a tsakanin 2009 zuwa 2010 a lokacin shi Oronsanye na rike da kujerar shugaban ma’aikata na Kasa.

Shi kansa Oransanye, a lokacin an gano cewa yana da mallakin asusun ajiya 66 da ake jibga masa kufin ƴan fansho na karya, ya tsuke baki yayi shiru.

Share.

game da Author