HARKALLAR DASUKI: Mun tofa wa Boko Haram addu’o’in naira bilyan 2.2 a Makka -Inji mai bada shaida

0

Wani mai bincike a Hukumar EFCC mai suna Adariko Micheal, ya yi zargin cewa an kashe naira bilyan 2.2 wajen hidimar yin addu’o’i a Najeriya da Saudi Arabiya, domin Allah ya kawo karshen Boko Haram a Najeriya.

Michael ya bada wannan shaida a matsayin mai bada shaida na farko (PW1), a shari’ar su Sambo Dasuki da ake yi a ranar Talata.

Dasuki shi ne Mashawarcin Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a Harkokin Tsaro.

Ana zargin sa da karkatar da dala bilyan biyu na kudaden sayen makaman yaki da Boko Haram.

Sauran wadanda ake tuhuma tare da Dasuki, sun hada tsohon Janar Manajan NNPC, Aminu Baba-kusa, Acacia Holdings Limited da kuma Reliance Referral Hospital Limited.

EFCC na tuhumar su da caje-caje har guda 32, wadanda su ka hada da cin amanar kasa, yin watandar makudan kudade da karbar makudan kudade ba bisa ka’ida ko izni ba.

A Babbar Kotun Tarayya ta Abuja, karkashin Babban Mai Shari’a Hussameini Baba-Yusuf ake yin shari’ar.

Lauyan EFCC Rotimi Jacobs ne ya gabatar da mai shaida, Micheal, wanda ya ce an danna naira bilyan 750 daga Asusun Musamman na Mashawarci Kan Tsaro, wato Dasuki zuwa asusun Referral Hospital Limited, daga First Bank aka tura kudaden.

Ya sake yin ikirarin cewa an sake tura naira bilyan 650 a asusun ajiyar Acacia Holdings Limited da ke EcoBank, yayin da aka sake tura naira milyan 600 da wasu naira milyan 200 wani asusun kamfanin da ke bankin UBA.

“Tsakanin ranakun 27 Ga Satumba, 2013 zuwa 16 Ga Afrilu, 2015, an tura wa Reliance Referral Hospital.

“Da mu ka tambayi daya daga cikin wadanda mu ka gurfanar din, wato Aminu Babakusa, sai ya ce mana an kashe kudaden wajen yi wa Najeriya addu’o’in kawo karshen Boko Haram.

“Da mu ka tambaye shi sunayen malaman da aka raba wa kudaden da lambobin wayoyin su, sai ya bada sunayen malami biyu kadai.”

Bayan ya zama saurare, sai Mai Shari’a Baba-Yusuf ya daga shari’a zuwa ranar 11 Ga Nuwamba.

Share.

game da Author