Gwamnonin Kudu-maso-Gabas sun jaddada himmar su ta karfafa hadin kan Najeriya

0

Gwamnonin Jihohin Kudu maso Gabas, jihohin da aka fi sani da jihohin kabilun Igbo, sun sake jaddada himmar su wajen ganin sun kara karfafa hadin kan Najeriya tare da ci cigaba da dunkulewar kasar wuri daya.

Sun jaddada haka a taron da su ka yi a Enugu, inda su ka ce lallai Nageriya ta ci gaba da kasancewa dunkulalliya shi ne mafi alheri a kasar nan, tare da kaunar juna, adalci da kuma rashin nuna son kai.

Wannan bayani na su na cikin wata takardar bayan taron da su ka gudanar din. A taron dai har da wakilai Gwamantin Tarayya ta tura.

Sun kuma yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi duba ga irin bukatu da korafe-korafen da ‘yan yankin kudu maso gabas ke yi.

Takardar Bayan Taron dai Gwamna David Umahi na Ebonyi ne ya karanta ta wa jama’a da manema labarai.

Umahi shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Kudu maso Gabas.

“Al’ummar Kudu maso Gabas sun yi amanna da kasancewar Najeriya kasa daya dunkulalliya.

” Kabilar mu ta yi katutu a kowane yankin kasar nan. Sun yi gine-gine, su na zaune lami-lafiya da al’ummar yankin da mutanen mu su ka je su na kasuwanci.”

Tawagar gwamnati na karkashin Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, Ibrahim Gambari.

Sauran sun hada da Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, dukkan ministocin yankin Kudu maso Gabas, sai kuma Sufero Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Adamu.

Shugabannin Kudu maso Gabas sun roki a tura dakaru su kutsa cikin surkukin dazukan su, domin a kamo Fulanin da ake yawo da zabga-zabgan bindigogi samfurin AK 47, su na tafka barna.

Sannan kuma sun jaddada cewa za su ci gaba da zaman amana tare da Fulanin da kiwo kadai su ka sa gaba, babu ruwan su kai hare-hare.

Sun yaba wa Buhari kan kokarin da ya yi wajen kawo karshen zanga-zangar #EndSARS. Kuma sun roke shi a hukunta batagarin da su ka maida zanga-zangar ta koma tarzoma.

Manya da kananan sarakunan gargajiyar yankin duk sun halarci taron.

Share.

game da Author