Kokarin da gwamnatin Buhari ke yi na kakaba wa soshiyal midiya takunkumi da dabaibayi, ya samu jinjina da goyon baya daga Gwamnonin Arewa.
Gwamnatin Buhari dai ta roki Majalisar Dattawa a kafa tsastsaurar dokar da za ta karya fukafukin soshiyal midiya.
Ministan Yada Labarai Lai Mohammed ya ce idan aka kyale soshiyal midiya babu takunkumi, to za su iya taewatsa kasar nan baki daya.
Sai dai kuma masu adawa da shirin na ganin cewa wannan dabara da tuggu ne kawai domin kirkiro hanyar dakile masu sukar gwamnati.
Cikin shekarar da ta gabata, Majalisa ta yi fatali da wani kudiri da wakilin APC ya gabatar da nufin kafa dokar karya fukafukin soshiyal midiya.
Takamaimen wadanda gwamnatin tarayya ta fi korafi a kan su, akwai Facebook, Instagram, WhatsApp da Twitter.
A ranar Litinin gwamnonin Najeriya sun nuna goyon bayan su ga karya fukafukin soshiyal midiya, ta hanyar kakaba masu tsauraran dokokin da su ka ce ta haka ne kawai za a iya dakile watsa labaran bogi da kirkirar karairayi ana watsawa cikin al’umma.
Kungiyar Gwamnonin Arewa sun nuna wannan goyon baya ne, a cikin wata takardar bayan taron da su ka fitar ga manema labarai a ranar Litinin, bayan tashi daga taron su da Sarakunan Arewa da sauran masu ruwa da tsaki.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, kuma Gwamnan Jihar Filato, Simin Lalong ne ya sa wa takardar hannu.
A taron, sun yi tsinkaye da nazari da tsokacin yadda a cewar su soshiyal midiya ke kara yada labaran bogi, kirkire-kirkiren karairayi, kad-da-kanzon-kurege da bayanan shifcin-gizo masu haddasa fitintinu a cikin kasa.
Discussion about this post