Yayin da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) ke ci gaba da yajin aiki tsawon watanni 10, ita kuma gwamnatin tarayya ta fara yi wa wata sabuwar kungiyar malaman jami’o’i rajista.
Ministan Kwadago da Ma’aikata, Chris Ngige ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja.
Ya yi bayanin ne a lokacin da shugabannin sabuwar kungiyar, mai suna ‘Congress of University Academics (CONUA) su ka kai masa ziyara.
CONUA ta kai ziyarar ce a karkashin jaforan ta Niyi Sunmonu.
An tattaro malaman jami’o’i na fadin kasar nan ne daga cikin malaman jami’o’in da ba su goyon bayan ASUU.
Ngige ya jajanta a kan yadda ASUU ke ci gaba da yajin aiki, tsawon watanni 10, ya na mai cewa hakan ya maida harkar ilmi baya sosai a kasar nan.
“Mu na murna da wannan ziyara da ku ka kawo a wannan ma’aikata. Domin mu na da iznin karbar bakuncin kowace kungiya, mai rajista ko wadda ba ta da rajista. Ku na da dama da ‘yancin da za ku nemi rajista, domin yin hakan, abu ne mai kyau.” Inji Ngige.
“Mu na da ‘yancin yin taron ganawa da ku. Saboda haka har ma mun fara shirye-shiryen yi maku rajista.
“Kun yi daidai da ku ka nemi a yi wa wannan sabuwar kungiya ta ku rajista. Wannan ma’aikata kuma ta yi daidai da ta fara bin matakan yi maku rajista.
“Na kafa kwamitin bin diddigin matakan yi maku rajista, yanzu kuma zan ce wa kwamitin ya hanzarta kammala nazarin takardun ku domin a yi maku rajistar da gaggawa.” Inji Ngige.
Ya kara da cewa an bai wa kwamitin makonni hudu ya kammala tsare-tsaren sa.
“Dama mu aikin mu a nan ya hada har da yi wa kungiyoyi rajista. Kuma aikin mu ne ganin cewa kungiyoyin da ba su aiki sun samu taimako daga wannan ma’aikata.
Tun farko jagoran kungiyar Sunmonu ya shaida wa Ngige cewa malaman jami’a daban-daban sai tururuwa su ke yi su na shiga sabuwar kungiyar, tun bayan kara ta a watan Fabrairu, 2018.
Ya ce sun kafa CONUA saboda sabani da bambanci tsakanin su ASUU ya ki ci, ya ki cinyewa.
Discussion about this post