Gwamnatin Kwara da gidauniyar Dangote za su tallafawa mata 15,000 a jihar

0

Gwamnatin jihar Kwara tare da hadin gwiwar gidauniyar Dangote za su raba wa mata 15,000 naira miliyan 150 tallafi domin su fara sana’a a kauyukan jihar.

Mai taimakawa gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq kan harkokin inganta al’umma Kayode Oyin-Zubair ya sanar da haka a garin Ilorin ranar Talata.

Oyin-Zubair ya ce za a baiwa kowace mace Naira 10,000 kafin karshen shekaran 2020.

Ya ce gwamnati ta yi haka ne domin inganta rayuwar mazauna karkara domin rage yawan cinkoson mutane a birane suma a can su kama sana’a ba sai sun yi tururuwa zuwa cikin birane ba.

Bayan haka gwamnati za ta hada hannu da hukumar ‘Forestry Research Institute of Nigeria (FRIN)’ domin samar wa mata irin kalwa domin suma a rika fafatawa da su wajen noma.

Ya ce gwamnati za ta shirya da gwamnatin kasar Kenya domin yin kasuwancin kalwan a kasuwannin kasar da wasu kasashe.

A ranar 28 ga Oktoba PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa gwamnatin Tarayya ta ba matan karkara 2,800 agajin kudi N20,000 kowaccen su a Jihar Zamfara a Shirin Bada Tallafin Kudi ga Matan Karkara, wato ‘Grant Project for Rural Women’.

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta sanar da haka tana mai cewa rabon kudin wani ɓangare ne na kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ke yi na cika alkawarin gwamnatin sa na magance matsalolin rayuwar jama’a.

Share.

game da Author