A wani takarda da aka raba wa manema labarai a garin Kaduna ranar Laraba Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin Gida Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnati ta janye dokar hana walwala a duk fadin jihar.
Aruwan ya ce jami’an tsaron da aka saka a sassan jihar za su ci gaba da aikin samar da tsaro.
A dalilin haka ya yi kira ga mutane da su kiyaye dokokin jihar cewa gwamnati ba za ta yi kasa–ƙasa ba wajen Kama duk wanda ya karya dokokin.
Gwamnati ta bada wadannan lambobin waya 09034000060, 08170189999 da mutane za su kira a duk lokacin da suka ga wani ko abin da bai kamata ba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin saka dokar hana walwala na awa 24 da gwamnatin Kaduna ta yi a Oktoba.
Hakan ya biyo bayan ta’addancin da wasu ƴan iska a jihar suka yi inda bayan fasa dakin ajiyar kayan tallafin Korona suka yi awon gaba da su.
A wancen lokaci Gwamnati ta ce yin haka ya zama dole domin kare mutane daga wadannan batagari da suka tada zaune tsaye a jihar.
Yadda ƴan iska suka farfasa dakin ajiyan abincin Tallafin Korona
A dalilin afkawa dakin ajiyar kayan tallafi na Covid-19 da wasu ‘Yan iskan gari suka yi a wasu sassan garin Kaduna, gwamnati ta saka dokar hana walwala na awa 24 a kananan hukumomin Kaduna ta Kudu da wasu sassan karamar hukumar Chikun.
Ƴan iskan gari tare da wasu mazauna unguwar sun far wa dakin ajiyan kayan tallafi na Covid-19 dake unguwar Barnawa, inda suka kwashe kayan dake ciki kaf, har da kofofi, da fitillu, kujeru da kwanufan rufin ginin.
Ba wadannan ƴan iska da suka far wa gidan ajiyan ba, har da mazauna unguwan duk sun fito sun kwashi rabonsu. Su ma sun bi sahun wadannan ƴan iska suna sace ajiyar gwamnatin.
Bayan haka sai wasu matasan daga unguwar Kakuri suka fara bi duk inda ake ajiye da wadannan kayan abinci suna farfasawa.
Gwamnatin jihar bata yi wata-wata ba sai ta saka dokar ta baci a yankunan da abin ya faru sannan aka aika da jami’an tsaro.
Discussion about this post