Gwamnatin jihar Kano za ta baiwa dalibai 60,000 ‘Yan asalin jihar tallafin karatu a wannan shekara.
Shugaban hukumar bada tallafin karatu ga daliban jihar Abubakar Zakari ya fadi haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano ranar Talata.
Zakari ya ce zuwa yanzu dalibai 50,000 sun cika fom din neman gwamnati ta basu tallafi.
Ya ce da farko gwamnati ta wadatar da fom 40,000 a yanar gizo domin daliban dake bukatan tallafin su cika amma daga baya ta kara yawan su zuwa 60,000.
An fara cike fom din a ranar 1 ga Satumba.
Bayan haka Zakari ya ce gwamnati ta ware sama da Naira biliyan 1.8 domin biya kudin makarantan dalibai ‘yan asalin jihar dake karatu a jami’o’in kasar nan sannan ta kuma ce za ta kara wa daliban yawan kudin alawus dinsu da take biya.
Daga Nan gwamnati ta ware Naira miliyan 700 domin biyan Kudin Makarantar dalibai ‘yan asalin jihar dake karatu a jami’o’in dake zaman kansu a kasar nan.
Sannan ta ware Naira miliyan 247 domin biyan Kudin makarantan dalibai ‘yan asalin jihar dake jami’o’in kasar nan.
Daga karshe Zakari ya ce gwamnati za ta ware Naira biliyan 1.7 domin biyan kudin makarantar daliban dake karatu a kasashen waje daga shekaran 2021.