Gwamnatin Gombe za ta fadada ayyukan samar da ruwan sha a jihar

0

Gwamnatin Jihar ta ware naira miliyan 250 domin ayyukan samar da ruwan sha na hadin guiwa a wasu kananan hukumomin jihar guda hudu.

Kananan hukumomin da zasu amfana da wannan aiki sun hada da Dukku, Kwami, Furnakaye da Balanga.

Kwamishinan yada labaran jihar, Ibrahim Kwami ya bayyana haka bayan ganawar kwamitin zartaswar jihar.

Bayan haka, kwamitin ta aminci a biya tarin bashin kudaden tallafin daliban jihar dake karutu a manyan makarantun kasar na tun shekaru hudu da suka wuce.

Daliban na bin jihar bashin kudin tallafin karatu na tsawon shekaru hudu da ba a biya su ba.

Gwamnati ta ware naira miliyan 112 domin biyan daliban. Haka zalika kuma an ware naira miliyan 204 domin biya wa daliban ajin karshe na babban sakandare kudin rubuta WAEC, NECO, da NABTEB.

Bayan haka kuma gwamnati za ta daga darajar wasu makarantu kuda uku dake shiyyoyi uku na jihar zuwa makarantu na zamani sannan kuma zata bunkasa ayyukan noma da samar da taki ga manoma.

A karshe kwamishina Ayyuka, Abubakar Bappah, ya bayyana cewa gwamnati ta soke kwangilar gina sabon tashan motocin hayan na jihar saboda rashin kwarewar kamfanin da aka ba a baya.

Bappa ya ce gwamnati ta ba kamfanin Triacta, wanda ta kware wajin yin ayyukan gine-gine na zamani domin cigaba da aikin.

Share.

game da Author