Ministan muhalli Muhammad Mahmood ya bayyana cewa gwamnati za ta cigaba da jaddada tsare-tsaren da ta ke yi don kawo karshen yin bahaya a waje a kasar nan.
Mahmood ya fadi haka ne a taron ranar amfanin ban daki ta duniya na shekarar 2020 da aka yi a Abuja a makon jiya.
Ya ce lokaci ya yi da za a dauki tsauraran matakai domin ganin an kawar da matsalar yin bahaya a waje a kasar nan.
Mahmood ya ce gwamnati a shekarun baya ta saka hannu a dokar iko domin hana yin bahaya a waje sannan ta saka dokar ta baci a fannin samar da ruwa da tsafta.
Ya ce ma’aikatar muhalli ta hada hannu da masana fasaha daga kasar India domin horas da ma’aikatan su hanyoyin kawar da matsalolin da ake fama da su a fannin samar da ruwa da tsafta.
Masana fasaha za su horas da ma’aikata 50 na ma’aikatar daga nan zuwa watan Disamba.
Bayan haka Mahmood ya ce ma’aikatar sa ta gina ban dakuna a fadin kasar nan sannan ta mika su ga gwamnatocin jihohin domin a rika kula da su.
Dagan Mahmood ya ce sauran matakan kawar da yin bahaya da ma’aikatar ta dauka za a fara amfani da su a duk kananan hukumomin kasar nan.
Ya yi kira ga masu ruwa da tsaki su mara wa gwamnati baya domin ganin ta cim ma burinta na kawar da yin bahaya a waje.
Discussion about this post