Gwamnati za ta ƙara wa malaman makaranta ladar koyarwa

0

Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu ya amince da sabbin tsare-tsaren da aka fito da su domin kara wa malaman makarantar kasar nan hanyoyin kara cin moriyar ladar koyarwar da su ke yi.

Ya ce tsarin koyarwa a kasar nan ya fuskanci matsaloli da yin wofi da shi da aka rika yi a baya, wanda hakan ya ce shi ne musabbabin tabarbarewar ilmi a kasar nan. Ya ce hakan ya sa ake yaye masu digiri a kasar nan, wadanda ba su san komai ba.

Adamu ya yi wannan bayani lokacin rantsar da Kwamitin Gudanarwa na Kasa, na wannan Shirin Farfado da Kulawar Malaman Makaranta a Najeriya, a ranar Alhamis a Abuja.

“Saboda sanin muhimmancin malamin makaranta wajen bunkasa ilmi mai nagarta da kuma bukatar rike kwararrun malamai ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da wasu tsare-tsaren inganta rayuwar malaman makaranta da kuma tsarin koyarwa gaba daya.”

Adamu ya ce hanya ta farko ita ce tsaurara ka’idojin dauka koyarwa, ta yadda za ta kasance sai zakakuri, mai hazaka, da kuma baiwa da kwarewa za a rika dauka.”

“Za a fito da tsarin matakan albashi na musamman ga malaman makarantun sakandire da makarantun koyon fasaha.

“Za a fito da alawus na mausamman ga malaman da aka tura koyarwa a yankunan karkata, alawus ga malaman koyar da kimiyya da sauran su.” Inji Minista Adamu.

Sannan kuma ya ce tilas a fito da takamaimen shekarar da ya kamata malamin makaranta ya yi ya na aikin koyarwa.

Baya ga shigo da tsarin fanshon malaman makaranta da za a yi, to kuma za a kayyade shekaru 65 ne wa’adin yin ritayar malamin makaranta. Ko kuma ya kasance shekaru 40 malamin makaranta zai shafe ya na koyarwa kafin ritaya.

Share.

game da Author