Gobara ta babbake gidaje 1,200 a jihar Barno

0

Akalla gidaje 1,200 ne suka kone kurmus a gobarar da ka yi a sansanin ‘yan gudun hijira dake kauyen Gajiram karamar hukumar Nganzai a jihar Barno.

Wannan ibtila’i ya faru ranar 24 ga Oktoba wanda akalla mutum 7200 sun rasa matsuguni.

Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar SEMA Yabawa Kolo ta sanar da haka tana mai cewa wannan ba shine na farko ba da hakan ke faruwa a wannan sansanin ‘yan gudun hijra.

Yabawa ta ce sansanin na yawan yin gobara saboda girke-girke da ake yi a waje kunna wuta a dakunan su.

Ta ce a ranar Lahadi hukumar ta rabawa mutanen da gobarar ya afkawa shinkafa, masara, wake, bargouna da gidajen sauro.

Sannan hukumar ta karbi gudunmawar kudi har naira miliyan Uku daga wajen sanatan da ke wakiltar Barno ta Arewa, naira miliyan 1.5 daga n Muhammed Monguno.

Ranar 15 ga Oktoba Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara yekuwar matakan rage faruwar bala’o’i a wuraren zaman jama’a da ma’aikatun gwamnati.

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya, Sadiya Farouq ta ce za a yi yekuwar ne don ƙara fakakar da kamfanoni da ma’aikatu da ma sauran jama’ar kasa game da yadda za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana tare da ɗaukar matakai don rage aukuwar bala’in gobara a dogayen benaye da gidajen masu yawan mutane da gine-gine mallakar jama’a da na gwamnati, da kuma wuraren aiki don tabbatar da cewa sun fito da tsarin ceton jama’a daga gobara tare da yin atisaye jefi-jefi kan yadda za a fice daga inda gobara ta barke.

Ta ce don tabbatar da hakan, wannan Ma’aikatar tare da hadin gwiwar hukumomin da aka dora wa alhakin kula da faruwar bala’o’i, za ta shirya atisaye na farko kan aikin ceto daga gobara a Ginin Sakatariyar Tarayya. Za a yi atisayen a ranar Juma’a, 23 ga Oktoba, 2020

Share.

game da Author