GIRMA YA FADI: Yadda Minista Malami ya kunyata Najeriya a gaban Kwamitin Bankin Duniya

0

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami ya kunyata tare da zubar wa Najeriya mutunci a gaban Kwamitin Bincike na Bankin Duniya (World Bank).

Ƴan kwamiti sun banƙaɗo yadda Malami ya lailayo karairayi ya kantara wa kwamiti. Hakan kuwa baya ga zubar wa Najeriya kima, har asarar dimbin kudi ya janyo wa kasar.

PREMIUM TIMES ta gano yadda Malami ya yi karin gishiri a bayanan sa a wata shari’a da aka tabka tsakanin Gwamnatin Tarayyar Najeriya da kamfanonin harkokin man fetur na ‘Interocian Oil Development Company da Interocian Exploration Company.

Wadannan kamfanoni biyu dai duk a birnin Delaware na kasar Amurka hedikwatar su ta ke. A can kuma su ke da rajistar su.

An gabatar da rikicin da ke tsakanin Najeriya da kamfanonin biyu a gaban Cibiyar Sasanta Sabani kan Hannayen Jarin Kamfanoni na Kasa da Kasa.

Wannan cibiya wadda aka kafa tun 1966, wato ICSID, Babban Bankin Duniya ne ke daukar dukkan dawainiyar ta, a Hedikwatar da ke Washington D.C, Amurka.

Yayin da ake yanke hukunci, kotun ta yi watsi da wasu ikirarin wuce-gona-da-iri da Minista Malami ya yi a madadin Najeriya.

Malami ya kantara karairayin Najeriya ta kashe wasu kudaden da ya nemi kotun ta sa kamfanonin biyu su biya. Amma daga baya an gano karairayi ne kawai ya shimfida.

A kan haka sai kotu ta ce hatta kudaden da ya kamata a rama wa Najeriya, wato adadin da ya kamata Malami ya ce su aka kashe, to ba a biya ba, tunda ya zabga karya.

A wurin shari’ar dai wasu fitattun lauyoyi ƴan Najeriya ne su ka wakilci kamfanonin biyu. Sun hada da Olasupo Shasore (SAN), Bello Salihu, Oba Nsugbe da Bimpe Nkontchou.

Ita kuma Najeriya, ta samu wakilcin manyan lauyoyi da su ka hada da Afe Babalola (SAN), Adebayo Adenipekun (SAN), Olu Daramola, Oluwasina Ogungbade, Ola Faro da sauran su.

Tankiya Tsakanin Najeriya Da Kamfanonin Amurka Biyu:

Kamfanonin hakar danyen mai na Interocian Oli Development Company da Interocian Oil Exploration Company, sun maka Najeriya kara a kotun ko kuma a gaban kwamitin, tun cikin 2013. Sun zargi Najeriya da karya alkawarin yarjejeniyar kwangila a tsakanin su.

An ba su lasisin hako mai a karkashin Lasisi mai Lamba 98 na ‘OML’ da kuma Lasisi Lamba 275 na “OPL”. Amma aikin hadin guiwa ne tsakanin su da NNPC da Pan Ocean Oil Company na Najeriya.

Sun rika hako gangar danyen mai 50,000 a kowace rana. Amma rikici ya fara tirnikewa tun a cikin 1998, lokacin da au ka ce su ke da hakkin mallakar kashi 40 bisa 100 na danyen mai da su ke hakowa a kullum a rijiya mai lamba 98 da mai lamba 275.

Sun kuma shaida wa kwamitin bincike cewa Najeriya na nunke su baibai, ta yadda ba su sanin duk abin da ake ciki kan barun harkokin kasuwancin danyen man da kudaden da ake tarawa.

A karshe dai kotu ta ce Najeriya ba ta karya ka’ida ba. Sannan kotun ta karkashin Mai Shari’a William Park, ta umarci kamfanonin biyu su biya Najeriya ramuwar dala 660,129.

Ana kammala shari’ar, bayan an yanke hukunci sai Malami ya buga sanarwar yadda Najeriya ta yi nasara a kan kamfanonin biyu.

Ashe jama’a ba su sani ba, akwai karairayin da Malami ys kantara wa kwamitin, inda ya yi ikirarin Najeriya ta kashe wasu kudaden da aka gano cewa karya ce kawai ya rafka.

Yayin da kamfanonin biyu su ka nemi kotu ta sa Najeriya ta biya su diyyar asarar da su ka ce sun yi ta dala milyan 4, 877, 463.12.

Shi kuma Minista Malami sai ya zabga wa kotun karya cewa ai Najeriya ce ma ya kamata kamfanonin su biya diyyar dala milyan 3,767,446.36.

A karshen bincike dai kwamiti ko kotu ta gano cewa kudaden da Malami ya ce Najeriya ta kashe, ko da an tattara an hada da kudaden biyan lauyoyi da sauran su, to bayanin Minista Malami ba gaskiya ba ne, zuki-ta-malle ce kawai. Don haka tilas Najeriya ta tashi dauke da buhun kunya ba tare da an biya adadin kudaden da Malami ya yi kintace ba.

Share.

game da Author