Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, tare da jami’an rundunonin tsaro na sojoji da ƴan sanda sun yi aikin sintiri a titin Kaduna-Abuja ranar Alhamis.
Wannan sintiri da suka yi ya kawo karshen labaran da ake ta yadawa wai matafiya sun kaurace wa Titin Kaduna-Abuja.
Baya ga bin tsawon titin da kwamishinan da tawagar sa suka yi, ya yada zango a cikin garin Akilubu, inda ya tattauna da shugabannin al’umma, na addini da na siyasa.
Aruwan ya roki mutanen gari da su taimakawa jami’an tsaro da bayanan sirri domin a samu nasarar cigaba da kakkabe su da ake yi.
” Kuna gani yanzu ba jiran su ake yi sai sun fito titi a fatattake su ba, jami’an tsaro har cikin daji suke bin su su tarwatsa su, hakan ya biyo bayan bayanai na sirri ne da suke samu. Ina kira da kuma ku taya su jami’sn tsaraon da duk wani taimako da za su bukata domin wannan aiki da suka saka a gaba.
Discussion about this post