Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci Dan Majalisar Tarayya Sani Galadima ya kai Faisal Abdulrashid Maina a kotun ko kuma a tura shi zaman kurkuku.
Honarabul Galadima mai wakiltar Karamar Hukumar Kaura Namoda, ya shiga wannan tsomomuwa ce bayan yq tsaya karbar belin Faisal, amma aka nemi Faisal sama da aka rasa.
Irin wannan tsomomuwa ce ta fada kan Sanata Ali Ndume, wanda ya tsaya wa Maina, amma a karshe Mai Shari’a Okon Abang ya tura shi kurkuku a ranar Litinin, saboda ya kasa gabatar da Maina a kotu, bayan ya karbi beli.
Abang, wanda ya tura Maina kurkukun Kuje, shi ne dai ya umarci Galadima ya kai Faisal kotu a ranar 4 Ga Disamba, ko kuma ya tura shi kurkuku, kamar yadda ya tura Maina.
Okong ya ce baya ga tura Dan Majalisa Galadima kurkuku da zai yi, kotu za ta kwace naira milyan 60 da ya ajiye kudin beli.
An dai bayar da Faisal beli cikin watan Disamba, 2019, yayin da ake tuhumar sa da laifin harkallar kudade tare da baban sa Maina.
Shi ma Ndume da aka tura kurkuku, an umarce shi ya kawo Maina ko kuma kotu ta kwace naira milyan 500 din sa da ya ajiye kafin belin Maina.
Sai dai Ndume ya daukaka kara ta hannun lauyan sa Marcel Olu, kuma ya nemi belin Ndume din a yau Laraba.
Amma Mai Shari’a ya ce an shigar da batun neman beli a makare, saboda haka sai gobe Alhamis.