Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya nada mahaifin tsohon gwamnan Kano kuma abokinsa na kud-da-kud kafin su raba jiha, daya daga cikin masu nada sabon sarki a masarautar Karaye.
Za a yi bukin nadin mahaifin Kwankwaso, Musa Saleh Kwankwaso, kuma Makaman Karaye, tare da sauran wadanda aka nada ranar Juma’a.
Sauran wadanda za anada sun hada da ‘Sarkin Bai’, Jibrin Ibrahim-Zarewa; ‘Sarkin Dawaki Mai-Tuta’, Bello Hayatu-Gwarzo; tsohon sanata, ‘Dan Iya’, Bashir Mahe; da ‘Madakin Karaye’, Ibrahim Ahmad.
Duk da cewa tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso basu ga maciji da gwamnan jihar, haka bai hana shi nada mahaifinsa wannan mukami ba.