Akalla mutum 20 aka gaggauta wa yin magani bayan sun kamu da cutar abinci mai guba, jim kadan bayan sun Kwankwadi kunun da aka yi geron da aka sace a dakin ajiya na taffin Korona.
Mutanen duk ‘yan cikin kauyen Joi ne da ke karkashin Karamar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.
Cikin wadanda su ka kamu da ciwon har da basaraken kauyen, Stephen Jogu. An ce a hannun wani mutumi aka sayo geron kwanaki kadan kafin kamuwa sa cutar.
Jugu wanda kuma shi ne Shugaban Mabiya COCIN, ya shaida cewa shi ma ya na cikin wadanda aka yi wa maganin cutar, tare da mutane 20.
“Na farka da tsakar dare na rika zawayi, washegari na gano ashe mu na da yawa. Mun fi mutum 20. Amma duk an sallame mu.
Wani mai suna Tim Danchal ya ce wasu da su ka sha kunun sun rika tsula zawayi, har sai da su ka suma.
Ya kara da cewa wasu har aman jini su ka rika yi. Amma dai duk an duba su.
Wani jami’in Lura da Cuta Mai Yaduwa, Livinus Miskoom, ya danganta cutar daga cin abinci mai guba wanda aka yi wasaso a Filato. Ya yi gargadin a guji cin irin wannan abinci.
An dai daka wasoson kayan abinci a wurare mallakar gwamnati da sauran jama’a. Ciki kuwa har da gidan tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara.