Farashin kayan abinci ya tashi a duniya watanni biyar a jere -Hukumar Abinci ta Duniya

0

Farashin kayan abinci ya tashi a fadin duniya cikin watan Oktoba. Wannan ya nuna farashin ya ci gaba da tashi kenan duk wata, har sau biyar a jere, daga Yuni zuwa Oktoba. Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ce ta fitar da rahoton, kuma ta bayyana haka.

Jadawalin Kididdigar Farashin Abinci da aka wallafa ranar Alhamis, ya tabo kasashe daban-daban inda aka tsakuro farashin wasu kayan abinci da su ka hada har da abincin gwangwanin jarirai (cereals), sukari, madara da man girke-girke.

Kayan abinci sun kara farashi da kashi 7.2 a watan Oktoba, fiye da tashin da farashin ya yi a cikin watan Satumba.

Wannan gagarimar matsalar tashin farashin kayan abinci a duniya, ta faru ne babu makawa sanadiyyar karancin alkamar da ake fitarwa waje daga kasashen Ajantina, da kuma rashin albarkar nomanvalkama da ba a samu sosai ba a wannan kakar a kasashen Turai ba da Amurka ta Arewa da kuma kasashen gabar Tekun Red Sea.

“Abincin da ake sarrafawa daga masara da kuma dawa ya kara farashi, amma kuma wanda bukatun da ake wa abincin da aka sarrafa daga shinkafa ya ragu a watan Oktoba.” Inji rahoton.

Rahoton ya kara da cewa farashin man ja da man waken soya ya yi gwauron tashin da watanni tara baya farashin su bai yi kamar na Oktoba ba.

Matsalar karyewar farashin mai da kuma yadda korona ta takwarkwashe kasashen Turai, ya haifar da rashin tabba a kasashen Turai din.

Farashin ‘cheese’ da na garin madara da na man butter’ ya karu da kashi 2.2 daga watan Satumba zuwa watan Oktoba.”

“Hauhawar farashin kayan abinci a duniya ya kara samun musabbabi ne daga bukatar kayan a kasashen Asia da Gabas ta Tsakiya.” Cewar rahoton.

Saboda karancin sukari daga Brazil da Indiya, hakan ya haifar da tashin farashin da kashi 7.6. Dama wadannan kasashen biyu su ne kasashen da su ka fi yin sukari a duniya.

Share.

game da Author