Majalisar Birtaniya ta nemi kasar ta kakaba wa shugabannin Najeriya da aka samu da laifin bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki, Lagos.
A zaman Majalisar na ranar Litinin, sun yi tattaunawa mai zafi kan Najeriya, inda wadanda su ka yi kakkausan bayanai kan zargin take hakkin jama’a, hana zanga-zanga ta lumana da bude wa masu zanga-zanga wuta, su ka nemi gwamnatin Birtaniya ta haramta wa shugabannin Najeriya shiga kasar, kuma ta kwace dukiyar duk wanda ke da hannu wajen tura sojoji su bude wa masu zanga-zanga ta lumana wuta a Lekki.
Wannan bayani na su ya biyo bayan wata takardar korafi ce ta e-mel da mutum 220,330 su ka sa wa hannu cewa su na goyon bayan Birtaniya ta kakaba wa Najeriya takunkumi.
Cikin wadanda su ka sa wa takardar hannu, sama da mutum 2000 ‘yan Najeriya ne mazauna Birtaniya.
Sun ce dabbaci ne da kuma azabtarwa a iske masu zanga-zanga sun yi dafifi a wuri daya, ba dauke da makamai su ke ba, amma a da sojoji su bude masu wuta.
A zaman Majalisar ta Birtaniya, an zauna a lokacin da mai kula da harkokin Afrika, Theresa Villiers ba ta nan.
Amma Mendy Morton ta tsaya a madadin ta, inda ita ma ta nuna bacin ran ta kan gwamnatin Najeriya, kuma ta ce tun a ranakun 21 Ga Oktoba da kuma 11 Ga Nuwamba, sun tuntubi Sakataren Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Enyeama, Gwamnan Lagos Babajide Sanwo-Olu da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.
Tuni dai kungiyoyi na cikin gida da wajen Najeriya ke ta kara matsa wa Gwamnatin Buhari lamba da nuna damuwa kan batun take hakkin dan Adam.
Duk da an rushe ‘yan sandan SARS, har yau Najeriya na fuskantar caccaka. Ta bayan-bayan nan, shi ne rahoton da gidan talbijin na CNN ya fitar, inda ya nuna bidiyon da CNN din ta ce tabbas sojoji sun bude wa masu zanga-zanga wuta.
An rika sa-toka-sa-katsi tsakanin sojojin Najeriya da Gwamnan Legas, inda kowa ya rika kokarin cire alkyabbar laifi daga wuyan sa, ya na ciki-cikin sakalawa kan wuyan dayan.
A na ta bangaren, Gwamnatin Najeriya ta aika wa CNN wasikar rashin amimcewa da rahoton da talbijin din ta nuna, cewa ta yi son kai, ba ta yi kuma kwakkwaran bincike ba.