EndSARS: Yadda za a kauce wa sabuwar zanga-zanga -Sanata Lawan

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya bayyana cewa ya kamata a samar wa dimbin matasa ayyukan yi a cikin Kasafin 2021, domin gudun sake barkewar wata zanga-zanga a kasar nan.

Lawan ya yi wannan jan hankali ne a ranar Litinin, lokacin da Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono ya bayyana a Majalisa domin kare Kasafin 2021 na ma’aikatar sa.

Sanatan ya ce samar da aikin yi ga dimbin matasan kasar nan, zai kawar da sake barkewar wata zanga-zanga a kasar nan.

“Ya kamata mu daina maganar abin da mu ka yi cikin shekarar 2020, nu maida hankali kan abin da za mu iya yi a 2021. Mun ga yadda zanga-zanga ta barke, wasu dalilan masu zanga-zangar nan, gaskiya su ka bayyana, ba karya su ka yi ba.

“Saboda haka tilas mu guji barkewar wata zanga-zanga ta hanyar kirkiro wa matasa ayyukan yi a cikin wannan Kasafin 2021 din nan.”

Lawan ya ce noma na daya daga cikin ginshikan samar da ayyukan yi ga dimbin jama’a. A kan haka ne ya ce ya zama wajibi a bai wa fannin noma muhimmanci.

“Man fetur ba ya iya samar wa kasar nan ayyukan yi. Mu tashi tsaye mu bunkasa harkokin noma domin abinci, tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.”

Idan ba a manta ba, Ma’aikatar Noma ta ce za ta ciwo bashin naira bilyan 459 domin bunkasa noma, tattalin arziki da samar da aikin yi ga matasa milyan biyar a cikin shekaru goma.

Kwamitin Harkokin Noma na Majalisar Dattawa ya umarci Minista Nanono ya je wurin Ministan Ilmi Adamu Adamu domin neman kudaden da Jami’ar Gona ta Zuru da ke Jihar Kebbi.

Share.

game da Author