#EndSARS: Yadda na shafe wata bakwai a kurkuku saboda na dauki ƴan sanda a taksi, na tambaye su kudin mota -Direban taksi

0

Wani direban taksi mai suna Mayowa Ayodele, ya bayyana wa kwamitin binciken cin zarafin da ƴan sanda su ka rika yi wa jama’a cewa, ya shafe watanni takwas kulle a kurkuku sakamakon sharrin da ƴan sanda su ka kitsa masa.

Ya ce sun yi masa haka ne kawai saboda ya dauke su a taksi, bayan ya gama zirga-zirga da su mai nisa, ya nemi su biya shi hakkin sa, to daga nan su ka maida hairi zuwa sharri.

Ayodele ya bayyana wa Kwamitin Binciken Cin Zarafin Da ‘Yan Sanda Su Ke Wa Jama’a mai zama a Abeakuta, babban birnin jihar Ogun haka a ranar Laraba.

Yadda Na Yi Wa Ƴan Sanda Alkhairi, Su Ka Rama Min Da Sharri -Ayodele

Ya shaida shaida wa kwamiti cewa wasu jami’an ‘yan sanda su hudu sun dauke shata a ranar 7 Ga Maris, 2018, ya kai su kuma ya maida su, amma su ka ki biyan sa.

Lokacin da ya nemi hakkin sa, sai su ka kama shi su ka kulle, daga nan su ka gurfanar da shi a kotu cewa sun kama shi ya na fara bututun mai da aka binne a karkashin kasa, domin satar ferur.

Jami’an ƴan Sandan da ya ce sun yi masa wannan sharri, su ne Buhari Yusuf, Ehimere Anthony da kuma wasu biyu da ya ce ba zai iya tuna sunayen su ba.

“Na dauke su daga Mowe zuwa Magboro. Daga can kuma na maida su Shagamu. Bayan sun sauka na tambayi kudi na naira 4,500, wadanda tun farko na ce hakan za su biya, kuma su ka amince.

“Amma maimakon su biya ni. Sai su ka ce ba za su biya ba, wai gwamnati su ke yi wa aiki. Da na tsaya ina ja-in-ja da su, sai babban su ya ce su kulle ni.”

Ayodele ya ce Ofishin MTD na Shagamu su ka fara kulle shi, kafin su maka shi kotu. Ya ce sai da ya shafe kwanaki 16 a kulle ofishin ‘yan sanda na MTD da ke Shagamu.

Daga nan an gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya ta Oke Mosan, Abeokuta da zargin ya na fasa bututun man fetur aka kama shi.

Ya ce daga nan mai shari’a ya sa aka tsare shi a kurkukun Oba cikin Abeokuta, inda ya shafe watanni bakwai a can.

Lauyan sa mai suna Kayode Aderemi, ya shaida wa kwamitin cewa an tuhumi Atodele tare sa wasu mutane takwas da laifin fasa bututu. Amma a karshe, duk kotu ta sallame su, saboda ba a same su da laifin komai ba.

“Bayan an sallame ni, na koma ofishin MTD na nemi a ba ni mota ta. Amma na samu wani sabon shugaba aka kai wurin. Ya rika yi min barazana, wai har ma karfin halin komawa zan yi a ba ni mota ta kenan?

Shi ma ya ce kawai a kulle ni.

Ya ce wannan mota da ya saya ya na biyan kudin da kadan-kadan, da ita kadai ya dogara. Ga shi kuma matar sa ta gudu, ta bar shi lokacin ya na tsare, saboda ‘yan sanda sun nuna wa duniya shi barawo ne.

Wadanda ya ke zargin dai ba su a kotun. Shi kuma Shugaban Kwamitin, Solomon Olugbemi, ya nemi Ayodele ya koma gaban kwamitin a ranar 30 Ga Nuwamba.

Share.

game da Author