#EndSARS: Yadda muka kubutar da Oba na Legas daga hannun ƴan jagaliya, muka ceto naira bilyan 2 daga bankuna -Sojoji

0

A daidai lokacin da ake korafi da ragargazar yadda sojojin Najeriya suka bude wa masu zanga-zanga wuta a Lekki, Lagos, Ahmed Taiwo, Kwamandan Bataliya ta 81 da ke Victoria Island Lagos, ya bayyana irin namijin kokarin da sojojin Najeriya su ka yi a lokacin tarzomar #EndSARS.

Ya yi bayanin a yayin da ya bayyana gaban Kwamitin Binciken Zargin Bude Wa Masu Zanga-zanga Wuta a Lekki.

Taiwo, wanda ya saka majigi, an nuno yadda bidiyon yadda ake kona ofisoshin ‘yan sanda, ake wa ‘yan sanda kisan-gilla, kona dukiyoyi da kuma nuno yadda masu tarzoma su ka rika cin naman babbakakkiyar gawarwakin wasu ‘yan sanda da aka banka wa wuta.

“Da yawan mu da mu ka rayu daga shekarun 1970s zuwa 2000s, mun ga yadda idan zanga-zanga ta wuce kwana uku, to batagari ke karbe ragamar ta, su maida ta mummunar tarzoma.

“Ni kai na na fada tarkon masu tarzomar nan. Wadanda su ka tare ni kai da ganin su ka san ‘yan iska ne rikakku, ba masu zanga-zanga ta lumana ba ne.

“To aikin sojoji ne su kai dauki idan matsala ta tsaro ta fi karfin ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.

” Gwamna Babajide Sanwo-Olu shi ya nemi sojoji su shiga tsakani, kuma abin da ya kamata kenan ya yi.” Inji shi.

Yayin da ya kunna bidiyon yadda aka yi ragaraga da Fadar Oba na Lagos, aka mamaye ta, ya ce Allah ya ceci ran sa basaraken yayin da sojoji su ka gaggauta kai dauki a fadar, su ka cece shi.

Ya ci gaba da bada labarin yadda sojojin suka kubutar da basaraken da iyalin sa, da kuma yadda aka yi kokarin karya kurkukun Ikoyi, amma sosoji su ka kai wa jami’an tsaron kurkuku, su ka hana karya kurkukun.

Sojoji sun kuma bada labarin yadda suka kubutar da naira bilyan 2 daga bankuna, wadanda ba don an yi gaggawar hakan ba, to da sai an wasashe kudaden ko an banka masu wuta.

Ya ce lokacin da su ka kama masu zanga-zanga, Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Tukur Buratai ya shaida masu cewa kada a timirmisa sa su, kuma kada a jibge su.

Share.

game da Author