#EndSARS: Sowore da wasu tsirarun abokansa sun dawo titunan Abuja domin cigaba da Zanga-zanga

0

Mawallafin jaridar SAHARA REPORTERS, Yele Sowore tare da wasu ƴan tsirarun abokan sa sun dira filin jirgin saman Abuja da hedikwatar ƴan sandan Najeriya da ke Abuja inda suka rika manna tambarin #EndSARS a titinan filin jirgin da titin hedikwatar ƴan sanda.

Sowore ya ce ba za a daina zanga-zangar ba har sai gwamnati ta canja salon mulki, an samarwa ƴan Najeriya duka abubuwan da suke bukata na jin dadin rayuwa kafin su janye daga tituna.

PREMIUM TIMES ta buga labarai da dama kan yadda masu zanga-zangar #EndSARS suka rika fitowa manyan titunan jihohin kasar nan.

Daga baya Zanga-Zangar #EndSARS sai ta koma banga-banga, inda Najeriya ta yamutse, aka rasa rayuka da dama da kadarorin kasa.

A jawabin da shugaba Buhari yayi a dalilin tarzomar da ya barke wa wannan lokaci, ya roki ƴan Najeriya su janye daka titunan kasar nan yana mai cewa gwamnati tana duba bukatun su kuma zata cika su duka.

An tafka asara masu yawa a sanadiyyar rubdugun ƴan iska suka rika yi wa ƴan sanda da kayan gwamnati da na jama’a.

Masu karatu da dama na ganin wannan wani sabon shiri ne don farfado da kurar da aka samu ta lafa.

Haka kuma ana na ana cigaba da binciken ainihin abinda ya auku a harin Lekki da ke Legas wanda ake zargin sojoji da bude wa masu zanga-zangar #EndSARS wura da yayi sanadiyyar mutane da yawa.

Share.

game da Author