#EndSARS: Masu zanga-zanga so su ka yi su kawar da shugabancin Buhari – IGP Adamu

0

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya yi ikirarin cewa masu zanga-zangar #EndSARS so su ka yi su kawar ko su tilasta wa Shugaba Muhammadu Buhari sauka daga mulki.

Adamu ya yi wannan kalami ne a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas, a lokacin da ake taron shugabannin yankin Kudu maso kudu da tawagar Shugaban Kasa. Kakakin yada labarai na Gidan Gwamnatin Ribas ne ya fitar da bayanin Sufeto Janar Adamu.

Adamu ya ce binciken asiri ya nuna an shirya zanga-zangar #EndSARS ce hususan don a kawar da Shugaba Buhari daga mulki.

Ya ce akwai kwararan masaniya cewa an rika daukar nauyin zanga-zangar daga cikin gida da kuma waje, domin a tada hargitsin da zai tilasta Buhari sauka.

Kakakin Yada Labarai na Gwamna Nyeesom Wike, wato Kelvin Eviri ne ya fitar da sanarwar.

“Adamu ya ce masu zanga-zangar so su ka yi su canja gwamnati a Najeriya, sannan kuma labaran boge su ka kara ruruta wutar zanga-zangar, har ya zama tarzoma.”

Sai dai kuma ba kamar yadda Adamu ya yi ikirari ba, su dai wadannan matasa da su ka yi zanga-zanga, abin da kawai su ka nema shi ne a soke ‘yan sandan SARS.

An rika samun tabarbarewar ‘yancin jama’a tun bayan da Buhari ya hau mulkin farar hula a 2015.

Ko a taro na farko da tawagar Buhari ta yi da gwamnonin Arewa, su ma cewa su ka yi zanga-zangar #EndSARS wani yunkuri ne na kawar da Buhari kan mulki.

A taron wanda aka yi a gaban Sufeto Janar Adamu, gwamnonin Arewa sun nemi a kakaba wa soshiyal midiya takunkumi, domin a cewar su, labaran bogi sun ruruta wutar zanga-zangar.

Amma kuma shugabanni da gwamnonin kudu ba su yarda cewa kokari ne na kifar da gwamnatin Buhari ba.

Shugabannin Kungiyar Kabilar Igbo Zalla, Ohaneze Ndi-Igbo, cewa su ka yi zanga-zangar #EndSARS, wani somin-tabi ne na wajibcin a sake fasalin tsarin mulkin Najeriya.

Taron da tawagar Buhari ta yi a Fatakwal, shugabannin yankin dai sun nemi a sauya fasalin Najeriya daga Federaliyya, yadda za a bai wa yankuna ko sassan kasa ‘yancin cin-gashin kai.

Gwamnonin Ribas, Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River da Edo duk sun halarci taron.

Akwai Ministocin yankin da su ka Kudu maso kudu duk sun halarta.

Ministan Harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi ne kadai daga ministocin yankin Kudu maso kudu da bai samu halartar taron ba.

Share.

game da Author