#EndSARS: Kisan da aka yi wa ‘yan sanda shedanci ne – El-Rufai

0

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana kisan da masu tarzoma su ka yi wa jami’an ‘yan sanda a zanga-zangar #EndSARS cewa shaidanci ne kawai.

Da ya ke hira da manema labarai bayan tashi daga taro, gwamnan na Kaduna ya ce ya zama wajibi al’umma su rika goyon bayan ga ‘yan sanda domin su rika gudanar da aikin su sosai da sosai.

Ya kara da cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu ya yi wa taron takaitaccen bayani kan tarzomar EndSARS da kuma abin da ya biyo baya.

“Mu na goyon bayan ‘yan sanda. Mun kuma yi amanna akwai batagari a cikin su, kamar yadda a kowane bangaren cikin al’umma ana samun batagari. Amma wannan ba zai taba zama hujjar da za a bin ‘yan sanda ana kashewa ba.

” Mun tattauna yadda za a karfafa tsaron al’umma a cikin lunguna da sako-sako, wadda wata hanya ce ta tabbatar da hada hannu da jami’an ‘yan sanda domin samun nasara a matakin farko.

“Kowa ya san kafa ‘yan sandan jiha ba abu ne karami ba a batun yi wa dokar kasa kwaskwarima. Saboda mun san da haka ne sai mu ka ce to bari my fara da matakin farko na tsaron yankunan karkara da lunguna a cikin al’umma tukunna.

“Don haka wadannan tsare-tsaren ‘community police’ ne za mu matsa gaba wajen kafa ‘yan sandan jihohi.” Inji El-Rufai.

Dangane da zanga-zanhar #EndSARS, gwamnan Kaduna ya ce, “Mun tabbatar masu hannu wajen shirya zanga-zangar su na da kyakkyawar manufa. Amma an samu akasi ‘yan iska da sauran ba’arin batagari su ka kwaje ragamar zanga-zangar.”

Share.

game da Author