#EndSARS: Hukumar Tara Haraji za ta yi wa kamfanoni da ‘yan kasuwa sassaucin kudaden haraji

0

Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida ta Kasa (FIRS), za ta yi sassaucin kudaden haraji ga kamfanoni, masana’antu da ‘yan kasuwar da su ka yi asara lokacin tarzomar #EndSARS.

FIRS ta ce za ta yi sassaucin ne domin tausaya masu kan gagarimar asarar da su ka yi sanadiyyar kona masu dukiyoyi.

FIRS ta bayyana wannan a matsayin wani tallafi da za ta yi wa jama’a domin rage masu radadin zafin asarar da su ka tafka.

Sanarwar ta ce za a sassauta karbar harajin can baya da ake bi bashi, wanda a baya aka ce a biya zuwa ranar 4 Ga Nuwamba, yanzu an kara tsawon wa’adin zuwa 31 Ga Disamba, 2020.

Sanarwar ta ce an kara wannan wa’adin ne ga kamfanoni da masana’antu da kamfanoni da ‘yan kasuwar da su ka shiga tasku sanadiyyar asarar dukiyoyi lokacin zanga-zangar #EndSARS da kuma wadanda su ka shiga kunci lokacin korona.

An kuma kara wa’adin karbar biyan bashin haraji da harajin-jiki-magayi daga ranar 21 na kowane wata zuwa ranar karshe ta kowane wata.

Sannan kuma masu biyan harajin da ke samun kudaden shiga da kudaden naira, amma su ke shan wahaka kafin su samu canjin kudaden waje, za su iya biyan harajin da ake bin su na haraji da kudaden naira.

“Sasaauta karbar harajin
abu ne da ya kamata a yi wa masu biyan harajin, domin taya su jimamin abin da ya faru na cikas din hada-hadar kasuwanci saboda korona, sai kuma asarar da su ka yi wajen tarzomar #EndSARS.”

Wani labarin mai kama da wannan kuma, cikin makon jiya ne PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed a Majalisar Dattawa ta na kaeyata zargin gwamnati za ta kara harajin-jiki-magayi.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa babu wani shiri da ake yi domin kara harajin-jiki-magayi, wato VAT.

Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed ce ta bayanna haka a lokacin da Kwamitin Harkokin Kudade ke sheka mata ruwan tambayoyi, ranar Alhamis, a Majalisar Dattawa.

Cikin 2019 ne Gwamnatin Tarayya ta kara kudin harajin VAT daga kashi 5% zuwa 7.5%. Wannan kari da aka yi ya sha suka daga akasarin ‘yan Najeriya, amma gwamnatin ta yi kunnen-uwar-shegu da korafe-korafen da aka rika yi.

Shugaban kwamitin ne Sanata Adeola Olamikekan, ya tambayi Minista Zainab ta yi bayanin halin kudirin Kudade na 2020 ke ciki, sannan kuma ya nemi jin gaskiyar lamari dangane da ji-ta-ji-tar da ake watsawa cewa za a kara harajin VAT.

Da ta ke bayani, Zainab ta ce babu wata magana mai kama da yiwuwar karin kashi 2.5% na harajin VAT da ake watsawa. Ta ce ba gaskiya ba ne.

Minista Zainab ta sha ruwan tambayoyi dangane da ganowar da sanatocin su ka yi cewa dukkan hukumomin da ke karkashin Ma’aikatar Kudi an yi masu kwangen kudade a cikin Kasafin 2021.

Sun buga mata misali da abin da su ka ce kudaden da aka ware wa Ofishin Akanta Janar, sun yi kadan sosai.

Akanta Janar Ahmed Idris a lokacin da ya ke kare kasafin ofishin sa, ya ce sun yi kadan matuka.

Baya ga naira bilyan 3.9 na kudaden ma’aikata, naira milyan 483 na manyan ayyuka, sai kuma naira milyan 752 na ayyukan yau da kullum.

Ahmed Idris ya shaida wa kwamiti cewa dukkan ofisoshi 37 da ke Ofishin Akanta Janar su na bukatar kwaskwarima.

Ya ce ofishin Legas kuwa katafaren gini ne, wanda idan aka kashe masa kudi aka gyara shi, to za a rika samun kudaden shiga idan aka bayar da hayar sa.

Ya koka a gaban kwamitin dangane da abin da ya ce wasu ‘yan kwakyariya da ‘yan baragada ne zaune a ginin.

Share.

game da Author