Gwamnatin Najeriya ta rubuta wa CNN wasika cewa ta sake nazarin rahoton da ta bada, inda ta nuna cewa lallai sojoji sun yi kisa a dandalin zanga-zanga a Lekki.
Wannan rahoto dai na CNN, Najeriya ta musanta shi, tare da cewa CNN ba ta yi adalci ba.
Yayin da Najeriya ta ce CNN ba ta iya aiki ba, su kuma ‘yan Najeriya sun yi ta sukar gwamnatin.
A cikin wasikar da Gwamnatin Najeriya ta aika wa Mataimakin Shugaban CNN, Jonathan Hawkins, Ministan Yada Labarai Lai Mohammed, ya bayyana cewa Najeriya na da ‘yancin daukar matakan shari’a a kan CNN, don gudun kada gidan talbijin din ya kara rura wutar zanga-zangar #EndSARS.”
“Domin magance matsalar, Najeriya na bukatar CNN ta sake yin wani sabon bincike don tabbatar da gaskiya shin an yi kisa ko ba a yi ba.
Lai ya ce wannan zai dora CNN a kan mizanin ko binciken su na farko da su ka yi, sahihi ne ko bai inganta ba.
“Amma abin da CNN ta yi a baya, ba ta tuntubi bangarorin da ya dace ba, sai ta yi hira da wadanda ra’ayin su ya zo daidai da na ta.”
“Don haka ya dace gidan talbijin na CNN ya ko dai ya wanke kan sa, ko kuma ya wanke bakin fentin da ya yi wa Najeriya, wanda kan iya rurutawa ko haddasa rudani matakamancin na da.”
Tuni dai aka kafa kwamitin bincike, wanda cikin wadanda su ka je bayar da shaidu, har da hukumar sojojin Najeriya.
Tuni dai Gwamnatin Majeiriy ta ce za a tabbatar an yi adalci ga dukkan wadanda ‘yan sanda su ka ci wa zarafi.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ce Majalisar Dattawa za ta tabbatar an bi hakkin dukkan wadanda ‘yan sandan Rundunar SARS da aka rushe su ka ci wa zarafi.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Abuja, Lawan ya kara da cewa Majalisar Dattawa za ta kara tabbatar da cewa dukkan alkawurran da gwamnati’ ta ce za ta cika wa masu zanga-zanga, ta cika su.
Ya ce alkawurran da su ka hada da gyara fasalin aikin dan sanda ta ingantacciyar gwamnati, duk za a cika su.
“Ina kara tabbatar wa matasa cewa Majalisar Dattawa za ta yi aiki tukuru tare da bangaren zartaswa domin a tabbatar an bi hakkin wadanda SARS su ka ci wa zarafi. Kuma sauran alkawurran da aka daukar masu duk za a aiwatar da su.
“Amma kuma ina kira matasa a guje daukar doka a hannu, domin mun jajirce cewa dukkan wadanda su ka ci zarafin jama’a za a hukunta su.
“Abin takaici ne yadda batagari su ka karbe akalar zanga-zangar #EndSARS, har su ke kai hare-haren lalata dukiya da kwasar kayayyaki.” Inji Lawan.
Lawan ya mika ta’aziyya ga iyalan jami’an tsaron da su ka rasa rayukan su a hannun masu zanga-zanga. Sannan ya ce za a kawo karshen barnar da batagari ke yi.
Ya ja kunnen matasa su guji daukar doka a hannu har su na lalata dukiyar gwamnati da wadda ba ta gwamnati ba.
Discussion about this post