#ENDSARS: Gwamnan Ondo ya koka da rashin ƴan sanda kan titinan Ondo

0

Yayin da kura ta lafa daga hargitsin da ya barke a kasar nan, bayan ‘yan takife sun kwace ragamar zanga-zangar EndSARS, Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo ya yi kukan rashin jami’an ‘yan sanda a kan manyan titinan Akure, babban birnin jihar.

Kukan Akeredolu na cikin wata takardar da Kwamishinan Yada Labarai na Ondo, Donald Ojogo ya fitar a ranar Juma’a, ya ce akwai bukatar jami’an tsaro su koma kan tirina, domin kare dukuya da rayukan Jana’a.

“Nazarin da aka yi a fadin jihar nan, ya nuna akwai matukar karancin jami’an tsaro, wanda hakan babbar barazana ce.”

Ya ce dole a samar da tsaro da kuma fahimta da amintaka tsakanin sannan kuma ya bada wa’adin kwanaki bakwai ga duk wani mai rike da makami ya damka shi ga hukuma, kafin wa’adin ya cika.

Akeredolu ya ce wa’adin na mako daya ya fara aiki ne daga ranar Juma’a, 30 Ga Oktoba.

Ya ce duk wani mai muggan makami a hannun sa, to ya gaggauta damka su ga Kwamandan Amotekun a ofishin sa da ke Alagbaka, Akure

Hukumar Kula da Aikin ‘Yan Sanda ta Kasa Police Service Commission), ta bayyana cewa za ta tilasta wa ba za ta tilasta wa jami’an ‘tan sanda komawa su ci gaba da gudanar da ayyukan su ba.

PSC ta bayyana haka cikin wata takarda da kakakin hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar wa manema labarai.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda zanga-zangar #ENDSARS ta rikide ta koma mummunar tarzomar da ta haddasa kashe ‘yan sanda 22, tare da banka wa ofisoshin su 205 wuta, wasu kuma aka ragargaza su.

An lalata dukiyoyi da kwashe dimbin wasu masu yawan gaske a garuruwa da dama.

Sanadiyyar bin su da aka rika yi ana kashewa da konewa a wuta, jami’an ‘yan sanda da dama sun ki komawa bakin aikin su a wasu garuruwan kasar nan.

Ba mu iya tilasta su, sai dai mu roke su da kuma lallami su daure su koma.

Cikin sanarwar da Ani ya saka wa hannu, ya ce “ba za su iya tilasta komawar
su aiki ba, saboda la’akari da yawan ‘yan sandan da masu tarzoma su ka kashe mana. ”

Ya kara da cewa hukunar PSC zaman makokin rashin jami’ai 22 da ta yi yayin tarzomar #ENDSARS.

“Wannan hukuma za ta tabbatar ana kara wa wa jami’an tsaron ta kwarin guiwar guiwar ci gaba da gudanar da ayyukan su.

“hukumar PSC na cike da bakin cikin rasa jami’ai 2.

Share.

game da Author