#ENDSARS: Ba za mu tilasta wa ƴan sanda yin gaggawar komawa kan aikin su ba -Jami’in PSC

0

Hukumar Kula da Aikin ƴan Sanda ta Kasa (Police Service Commission), ta bayyana cewa za ta tilasta wa ba za ta tilasta wa jami’an ƴan sanda komawa su ci gaba da gudanar da ayyukan su ba.

PSC ta bayyana haka cikin wata takarda da kakakin hukumar, Ikechukwu Ani ya fitar wa manema labarai.

An fitar da wannan sanarwa ne bayan wata jarida ta buga labarin cewa hukumar PSC ta ce za ta fara korar ‘yan sandan da su ka ki komawa wurin aiki.

PSC ta ce wannan labari karya ce, hukumar ba ta ce za ta kori kowa ba.

PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda zanga-zangar #ENDSARS ta rikide ta koma mummunar tarzomar da ta haddasa kashe ‘yan sanda 22, tare da banka wa ofisoshin su 205 wuta, wasu kuma aka ragargaza su.

An lalata dukiyoyi da kwashe dimbin wasu masu yawan gaske a garuruwa da dama.

Sanadiyyar bin su da aka rika yi ana kashewa da konewa a wuta, jami’an ‘yan sanda da dama sun ki komawa bakin aikin su a wasu garuruwan kasar nan.

Ba mu iya tilasta su, sai dai mu roke su da kuma lallami su daure su koma.

Cikin sanarwar da Ani ya saka wa hannu, ya ce “ba za su iya tilasta komawar
su aiki ba, saboda la’akari da yawan ‘yan sandan da masu tarzoma su ka kashe mana. ”

Ya kara da cewa hukunar PSC zaman makokin rashin jami’ai 22 da ta yi yayin tarzomar #ENDSARS.

“Wannan hukuma za ta tabbatar ana kara wa wa jami’an tsaron ta kwarin guiwar guiwar ci gaba da gudanar da ayyukan su.

“hukumar PSC na cike da bakin cikin rasa jami’ai 2.

Share.

game da Author