EFCC za ta tono ramukan da aka binne naira bilyan 4.6 a kan idon Minista Fashola

0

Hukumar EFCC ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa za ta binciki yadda aka yi harkalla, wuru-wuru da jidar zunzurutun naira bilyan 4.6 a Ma’aikatar Samar da Wutar Lantarki a karkashin Minista Babatunde Fashola, a cijin 2019.

Kakakin EFCC Wilson Uwujaren ne ya shaida wa wannan jarida haka a ranar Laraba, bayan da ta fallasa yadda aka karkatar da kudaden ta hanyar yi wa ma’aikatan ma’aikatar watandar kudaden a asusun ajiyar su na bankuna daban-daban.

Bayanan EFCC

A matsayin mu na hukumar da ke kan gaba wajen yaki da wawurar kudade, ba za mu kauda kai ga wannan labarin karkatar da kudade da aka fallasa ba.” Haka Uwujaren ya shaida wa wakilin mu.

Ya kara da cewa duk da dai EFCC ba ta da cikakken bayanan yadda aka rika kwasar kudaden, za ta kara nazarin rahoton da aka buga na wawurar kudaden.

Sai dai bai ce ga lokacin da za su bayyana binciken da za su yi ba, bayan sun kammala.

PREMIUM TIMES HAUSA ta fallasa yadda ma’aikatar Fashola ta kacaccala wa ma’aikatan ta naira bilyan 4.6, kowa ya yi gum da bakin sa.

Binciken ya bankado cewa tsakanin watan Satumba zuwa Disamba na 2019, an sungumi zunzurutun naira bilyan 4.6 na Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje aka rika gabza ana tutturawa asusun ajiyar banki na wasu daraktoci da ma’aikatan da ke ma’aikatun uku.

PREMIUM TIMES ta tabbatar da haka a wani binciken kwakwaf da ta yi. Kuma ta mallaki takardun da su ka tabbatar da cewa tuttura kudaden duk harkalla ce.

PREMIUM TIMES ta tura wa Ma’aikatar Makamashi, wato hasken lantanki wasikar neman rekod din kidaden da aka tura. Amma sai aka amsa da cewa naira milyan 157 ne kadai aka tura a Asus use mutane 127.

Sai dai kuma kwafe-kwafen takardun bayanan sa ke hannun PREMIUM TIMES, ya tabbatar ce karya ma’aikatar ke yi.

A yanzu dai Ma’aikatar Makamashi ita kadai ta ke, an cire ta karkashin rukunin ma’aikatun da ke karkashin Minista Raji Fashola, aka nada mata Minista Sale Mamman.

Amma dai a lokacin da aka gabji makudan kudaden aka yi watanda da su, ma’aikatar makamashi wato lantarki, a hannun Fashola ta ke.

Yadda Mutum 21 Su Ka Jide Naira Bilyan 4.6

Rekod din da PREMIUM TIMES ta samu a Rumbun Tattara Bayanan Kidade (Open Treasury Portal), ya nuna cewa an daddatsa kudaden har gida 654, duk aka tura cikin asusun mutum 21.

Kashi 2 bisa 3 na kidaden duk mutum 2 aka tura wa su: Ogueri Ugochukwu Pascal da wani mai suna Olasehinde Micah.

An loda naira bilyan 1.6 asusun Pascal (N1,642,4407,539.93). Ba lokaci daya aka gabza masa kudin ba. Daddatsa kudin aka yi, aka rika tura masa har su 306.

Shi ma Micah an tura masa naira bilyan 1.4 (1,417,921,892.59). Shi kuma sau 34 aka tura masa kudaden.

Akasarin kudaden an tura su ne tare da bayanan abin da aka yi da kudaden. Amma bayanan daga na bige, gidoga sai na bad-da-bami.

Share.

game da Author