Duk da durkushewar tattalin arziki, Najeriya ce ke kan gaba a bunkasar tattalin arziki a Afirka – Wakilitar Birtaniya

0

Wakiliyar Kasuwanci ta Birtaniya a Najeriya, Helen Grant, ta bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi saurin bunkasa a Nahiyar Afirka duk da ruftawa cikin halin karyewar tattalin arziki.

Grant ta fadi haka ne a taron kwana biyu na harkar saka jari na kasashen waje (NDIS) wanda hukumar kula da kasashen waje ta Najeriya (NiDCOM) ta shirya, tare da hadin gwiwar wata kungiya mai zaman kanta ta Najeriya (NDSI).

Taron, wanda shine karo na uku, an fara shi a ranar 20 ga Nuwamba kuma zai kammala shi a ranar Asabar.

An yi wa taron na wannan shekara taken, ” Bunkasa Tattalin Arziƙi bayan annobar Korona: Hadin gwiwar saka jari daga ƴan Najeriya mazauna kasashen Waje”.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) da ke aiko da rahotanni game da abinda ke gudana a wajen taron ya shaida cewa, Grant ta ce za ta karfafa alakar Birtaniya da Najeriya wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.

Ta ce gwamnatin Birtaniya a shirye take ta ilmantar, sannan kuma ta yi koyi da, Najeriya ta hanyar inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Ta kara da cewa Birtaniya da Najeriya suna da matukar abin da ya hada su, musamman a bangaren al’adu da yare, kuma ta jaddada bukatar gina irin wannan dangantakar da ke akwai don kawo ci gaban tattalin arziki.

Ta ce Najeriya na cike da damarmakin saka jari da dama da na cigaban arzikin kasa.

” Muna sa ran za mu dawo Najeriya don gano hanyoyin kasuwanci masu inganci da gwamnatin Birtaniya za ta iya hada hannu da su wajen samar da fa’idodi na zahiri da na dogon lokaci don cigaban kasashen biyu ” Kamar yadda ta ce.

Share.

game da Author