Gwamnan Jihar Ribas Neysom Wike ya bayyana cewa Dokar Musamman (Executive Order 10) mai lamba 10 da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wadda ta bai wa Gwamnatin Tarayya ikon kamfatar kudade daga asusun jihohi ta na bai wa bangarorin shari’u da kotunan jihohi, dokar karfa-karfa ce, wadda ba za ta zame wa dimokradiyya alheri ba.
Yayin da ya ke jawabi a Taron Shekara-shekara na Nazarin Dokokin Manyan Laifuka, Wike ya ce ba wani abin alheri ne gwamnatin APC ta kulla ba, sai shirye-shiryen tuggun zabe a 2023 kawai.
Ya ce an ga zabe ya zo shi ya sa gwamnatin Buhari ta wanzar da dokar domin bai wa kotunan jihohi ‘yancin su daga gwamnatin jihohi, amma kuma a lokaci guda za su koma “amshin Shatan gwamnatin tarayya.
” Don ka kafa kotuna amma ba ka sakar masu mara yadda za su yi adalci ba, kamar yadda dokar kasa ta tanadar, ai babu maganar adalci da ‘yanci kenan.” Inji Wike, a wurin taron wanda Gidauniyar Jaddada Sahihiyar Turbar Doka da Oda (Rule of Law Development Foundarion) ta shirya a Abuja.
Da ya ke magana a kan tsaro, ya ce ba a bukatar sai an yi wa dokar kasa kwaskwarima sannan jihohi za su iya kafa jami’an sa-kai da za su rika taimaka wa sauran jami’an tsaro wajen samar da tsaro a jiha.
” Ƴan sandan Najeriya su 372,000 kacal ba za su iya sa-ido a kan ‘yan Najeriya su milyan 195 ba.”
Ya yi korafin yadda ake nuna bambanci a kasar nan, inda ya ce yayin da wasu jihohi ke kafa jami’an tsaron su, ita ma Ribas ya kafa a karkashin dokar jiha ta 2018.
Ya ce abin mamaki, abin al’ajabi da takaici, sojoji sun hana a fara horas da jami’an tsaron.