Yawan bukatar da masu amfani da albasa ke yi, ambaliya da kuma matsalar ingantattun wuraren ajiya su ne dalilin da ya sa farashin albasa ya yi tashin-gwauron zabi a Najeriya. Binciken PREMIUM TIMES ne ya tabbatar da haka.
Sai dai kuma wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar, ya tabbatar da cewa farashin albasa ya yi matsanancin tashi, tare da karancin albasar ita kan ta, dalilin tarzomar da ta barke sanadiyyar zanga-zangar #EndSARS a kudancin kasar nan.
An yi zargin kashe wasu ‘yan Arewa a jihohin Kudu-maso-Gabas da Kudu-maso-Kudu, tare da kona dukiyoyin su. Wannan ya sa wadanda abin ya shafa sun rika watsa bayanai da hotuna a shafukan soshiyal midiya, su na cewa kada ‘yan kasuwar kayan abinci su sake su kai nau’o’in kayan miya a kudu.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin wasikar korafin da Majalisar Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ta rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da kuma Babban Daraktan Hukumar SSS na Kasa, inda ta nuna damuwa kan kisa da barnar dukiyar da ta ce an yi wa Musulmi a kudancin kasar nan, a lokacin tarzomar #EndSARS.
A yau a fadin Najeriya farashin albasa ya yi tashin-gwauron-zabi, har ta na neman gagarar talaka a wasu garuruwa, musamman a kudancin kasar nan.
A baya farashin ya dan fara tashi ne kadan, bayan a dade cak a tsaye wuri daya. To kuma lokaci daya a kusan karshen watan Oktoba zuwa cikin Nuwamba, sai farashin ya yi sama, fiye da karfin aljihun talaka.
Tuni dai jama’a ke ta shiga soshiyal midiya su na korafi, tare da tura hotunan ‘yar kadan din albasar da su ka saya da yawa a farashi mai tsadar gaske.
Farashin buhun albasa ya nunka sau 2 ba ma sau 1 ba a wasu garuruwa ko jihohi 5 a Najeriya.
Karin ya shafi kasuwanni a Ekiti, buhun da ake sayarwa N18,000 yanzu ya kai naira N58,000.
Wata mata mai suna Angela, ta ce “a yanzu albasar naira 100 ba za ta ishe ni yin girki ba. Wannan da ka ke gani a hannu na, naira 500 na saye ta. Amma a baya naira 100 ta ke kacal.”
Albasa ta yi karanci a kasuwar Oko da ke Asaba, Jihar Delta. Wadda ake dan iya samu kuma ta yi masifar tsada.
An tabbatar wadda a baya ake saye naira 25,000 yanzu ta kai naira 70,000.
Buhun naira 15,000 a kasuwar Dei Dei da ke Abuja, yanzu ya kai naira 40,000 zuwa naira 42,000.
A kasuwar Anacha kuwa ta naira 22,000 yanzu ta kai naira 70,000.
Haka abin ya ke a Jos jihar Filato da jihar Ondo.
An dai fi noma albasa a jihohin Kano, Kaduna, Sokoto, Jigawa, Filato, Bauchi da Kebbi.
Discussion about this post